Gwamna a Arewa Ya Yi Nasara, An Kama Mutum 1,000 Masu Taimakawa Ƴan Bindiga
- Gwamna Dikko Radda ya ce dakarun rundunar tsaron da ya ƙirƙiro sun kama ƴan leƙen asiri akalla 1000 masu taimakawa ƴan bindiga a Katsina
- Malam Dikko Raɗda ya ce gwanatinsa ta gano tushen matsalar tsaron jihar kuma ta maida hankali wajen magance su
- Ya bayyana haka ne da ya karɓi bakuncin shugaban rundunar sojin saman Najeriya, ya ce gwamnatinsa a shirya take ta taimakawa sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana cewa rundunar ƴan sa'kai (CWC) da ya kafa a Katsina ta kama ƴan leken asiri 1000 da ke aiki da ƴan bindiga.
Gwamna Raɗɗa ya ce waɗanda aka kama da aka fi sani da infoma, an gano suna aiki da ƙungiyoyin ƴan bindiga daban-daban a faɗin jihar Katsina.
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi baƙuncin babban hafsan rundunar sojin saman Najeriya, Hassan Abubakar, Leadership ta rahoto.
Gwamna Dikko ya bukavi haɗin kan sojoji
Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) wajen dakile ayyukan ‘yan fashin daji.
Gwamnan ya kuma ba rundunar sojin tabbacin cewa gwamnatinsa a shirye take ta tallafa musu ta kowace hanya suke buƙata domin dawo da zaman lafiya.
Dikko Radda ya bayyana irin ci gaban da aka samu wajen ganowa tare da cafke infomomin ‘yan bindiga, inda ya bayar da misali da rawar da dakarun CWC na Katsina suka taka.
Ya kuma kara da cewa gwamnati ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin domin gano tare da kawar da ‘yan bindiga daga doron duniya.
Gwamnan Katsina zai magance tushen matsalar tsaro
Bugu da kari, gwamnan ya ce sun gano cewa rashin aikin yi, jahilci, da fatara ne ke haifar da kalubalen tsaro a jihar Katsinan Dikko, rahoton Punch.
A cewar Raɗɗa, akwai bukatar magance tushen matsalolin, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ninka kokarinta domin cimma wannan buri.
Gwamnan ya ce gwammatinsa ta haɗa kai da sarakuna, malamai da shugabannin al'umma domin zaƙulo miyagu da yin maganinsu a kauyuka.
Mahara sun kashe sojoji a titin Funtua-Gusau
A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun kai hare-hare a kan titin hanyar Gusau zuwa Funtua da safiyar ranar Alhamis, 12 ga watan Satumban 2024.
Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutum bakwai ciki har da sojoji guda uku masu yi wa injiniyoyi ƴan ƙasashen waje rakiya.
Asali: Legit.ng