Ambaliyar Maiduguri: Shugaba Tinubu Zai Nema wa Jama'a Taimako, Ya Kafa Asusun Tallafi

Ambaliyar Maiduguri: Shugaba Tinubu Zai Nema wa Jama'a Taimako, Ya Kafa Asusun Tallafi

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnatin jihar Borno bisa iftila'in ambaliya a Maiduguri
  • Shugaban ya bayyana takaicin halin da jama'a a jihar su ka shiga bayan afkuwar ambaliyar da ta kashe rayuka
  • Tinubu ya kuma bayyana kafa asusun tallafa wa mutanen da iftila'i ya shafa a fadin kasar nan domin saukaka masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kafa asusun tallafa wa mutanen da iftila’in ambaliya ta shafa a jihar Borno.

Ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar gani da ido Maiduguri bayan an samu mummunar ambaliya da ta kashe sama da mutum 37.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Dattijon attajiri, Dantata ya tallafa wa Borno da sama da Naira biliyan 1

Bola Ahmed
Shugaban kasa ya kafa asusun tallafa wa yan Maiduguri Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugaban ya jajanta wa gwamnati da al’umar jihar Borno bisa mummunar ambaliyar, tare da neman masu dukiya su agaza wa jama’ar da iftila’in ya shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya: Tinubu ya nemi agajin masu kudi

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nemi daukin masu kudi a kasar nan wajen tallafa wa wadanda ambaliya ta shafa.

Ya kara da cewa jama’a su na cikin yanayi mara dadi, ga kuma rashin tabbas da yanayin ke ciki zai iya ta’azzara matsalar.

Majalisa za ta taimaka bayan ambaliya

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio wanda ya raka shugaban kasa zuwa Maiduguri ya ce za su ba da gudunmawarsu.

Ya dauki alkawarin hada kai da gwamnatin tarayya wajen samar da asusun da zai kawo wa jama’ar Maiduguri saukin iftila'in.

Ambaliyar Borno: Shugaba Tinubu ya jajanta

Kara karanta wannan

'Ka da mu zargi kowa': Tinubu ya bayyana abin da ya jawo ambaliyar Maiduguri

A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci jihar Borno jim kadan bayan ya dawo Najeriya domin jajanta wa gwamna Babagana Umara Zulum bisa iftila'in ambaliya.

A ranar Talatar da ta gabata ne aka samu mummunan ambaliya a Borno bayan ruwa ya haura madatsar ruwan Alau, har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 37 a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.