Ana Murnar Kisan Ubangidan Turji, Gwamna Ya Ƙara Tona Badaƙalar Ministan Tinubu
- Gwamnan Zamfara ya ce bai taras da ko kwabo a baitul mali ba lokacin da ya karɓi mulki daga Bello Matawalle a watan Mayu, 2023
- Dauda Lawal ya ce EFCC ta yi zargin sace N70bn amma yana shiga ofis ya gano kuɗin da suka ɓata a mulkin Matawalle sun haura N250bn
- Matawalle, wanda a yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaro ya sha musanta zargin y iwa baitul-malin Zamfara tatas da yake kan mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce ko kwandala bai taras a baitul-mali ba lokacin da ya karɓi mulki daga magabacinsa, Bello Matawalle.
Gwamna Lawal ya ce lokacin da ya shiga ofis, ya gano cewa sama da N250bn ne suka yi ɓatan dabo ƙarƙashin mulkin tsohon gwamnan.
Dauda Lawal ya yi wannan furuci ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv cikin shirinsu na 'siyasa a yau' ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Lawal ya sake taso Matawalle
Ya ce kafin ya karɓi ragamar mulki, ya ji hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta fara bincike kan satar N70bn amma da ya shiga ofis sai ya gane wannan ba komai ba ne.
"A wani lokaci a watan Mayu, 2023, hukumar EFCC ta yi zargin satar N70bn tun kafin na karɓi mulki. Da na shiga ofis sai na gane N70bn ɗin da suka ambata wasan yara ne."
"Bisa bayanan da muka tattara sama da N250bn sun ɓata, abin kamar wasan barkwanci. Bari ku ji yada na gaji Zamfara, lokacin da na karɓi mulki babu N4bn a asusu, ba ko sisi."
"Ma'aikata na bin bashin albashin watanni uku, shekaru uku babu wani ɗan Zamfara da ya rubuta WAEC da NECO. Haka na biya bashin N1.3bn na WAEC da N1.6hn na NECO."
- Dauda Lawal.
Gwamna ya jaddada matsayarsa kan ƴan bindiga
Gwamnan ya kara da cewa tun da ya hau mulki bai taɓa bai wa ƴan bindiga ko kwabo ba, kuma ya jaddada cewa ba zai tsaya ɓata lokacin tattaunawar sulhu da su ba.
Matawalle, wanda yanzu shi ne karamin ministan tsaro, ya sha musanta yi wa baitul-malin Zamfara ƙarkaf kafin ya sauka daga mulki, in ji Daily Trust.
Gwamnan Zamfara ya faɗi ƙarshen Bello Turji
A wani rahoton kuma Gwamna Dauda Lawal Dare na Zamfara ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci a jihar baki daya nan kusa.
Dauda Lawal ya ce yana da tabbacin an kusa kawo karshen kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng