Gwamna Dauda Ya Fadi Halin da Turji da Yan Bindiga Ke Ciki bayan Kisan Halilu Buzu

Gwamna Dauda Ya Fadi Halin da Turji da Yan Bindiga Ke Ciki bayan Kisan Halilu Buzu

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta yi magana game da halin da ake ciki musamman bayan kisan Halilu Sabubu watau Buzu
  • Gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya ce ya fi kowa farin ciki game da halin da ake ciki yanzu kan ayyukan ta'addanci
  • Wannan martani na zuwa ne bayan hallaka Sabubu da rundunar sojoji suka yi a ranar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya nuna farin cikinsa game da kisan Halilu Sabubu.

Gwamnan ya yabawa jami'an tsaro game da kokarin da suka yi na kawo karshen kasurgumin dan bindiga.

Gwamna Dauda Lawal ya nuna jin dadi kan kisan Halilu Sabubu
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya bayyana cewa yan bindiga sun rikice a jihar. Hoto: Dauda Lawal.
Asali: Twitter

"Bello Turji ya rikice yanzu" - Gwamna Dauda

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi lokacin gamawa da Turji, ya tona abin da ke rura wutar

Dauda Lawal ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Litinin 16 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dauda Lawal ya ce yanzu haka Bello Turji da sauran yan ta'adda sun rikice bayan kisan Sabubu.

Ya ce duk sauran yan ta'addan ba su da jajaircewa kamar yadda Sabubu ya ke da shi.

Ta'addanci: Gwamna Lawal ya nuna farin ciki

"Ina daga cikin wadanda suka fi farin ciki game da halin da ake ciki a Zamfara kan ta'addanci."
"Kamar yadda ka sani Sabubu na daga cikin hatsabiban yan ta'adda da ke addabar al'umma musamman a Arewacin Najeriya."
"Abin ya sauya yanzu saboda mabiya Sabubu ba su da kwarin guiwa kamarsa, a yanzu haka duk sun rikice ciki har da Turji."

- Gwamna Dauda Lawal Dare

Gwmanan ya ce kisan Sabubu ya kawo kwanciyar hankali a Zamfara da makwabtanta.

Kara karanta wannan

Jerin rikakkun yan ta'adda 7 da gwamnatin Tinubu ta yi nasarar hallakawa

Gwamnatin Tinubu ta hallaka manyan yan ta'adda 7

Kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi nasarar hallaka kasurguman yan bindiga da dama wanda suka addabi al'umma musamman a Arewa maso Yamma.

Tun bayan hawan gwamnatin, ta samu nasarar hallaka mafi yawan kasurgumai kuma shugabannin yan ta'adda da dama.

Hakan bai rasa nasaba da jajircewar kami'an tsaro wanda a yanzu haka sun tare a yankin Arewa maso Yamma domin yaki da yan ta'adda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.