Jerin Manya da DSS Ta Cafke da Cin Zarafi da Suka Jawo Cece Kuce a cikin Mako
Abuja - Yan Najeriya da dama sun caccaki hukumar tsaro ta farin kaya, DSS kan cin zarafin al'umma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
A cikin mako daya, hukumar ta kama manyan mutane da dama a kasar tare da cin zarafin al'umma.
Ayyukan DSS a cikin mako guda
Bayan dira a ofishin SERAP, hukumar ta kuma cafke shugaban NLC, Joe Ajaero da wasu mutane. Bayan dira a ofishin SERAP, hukumar ta kuma cafke shugaban NLC, Joe Ajaero da wasu mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta duba mutanen da DSS ta kama da ake ganin cin zarafi ne.
1. Joe Ajaero
Hukumar DSS ta cafke shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero a filin tashi da saukar jiragen sama.
Kama Ajaero ya jawo ka-ce-na-ce da ake ganin cewa ana neman rufe bakin kungiyar ne bayan karin farashin mai.
Daga bisani, kungiyar ta yi barazana tare da ba gwamnati wa'adi zuwa 12 na dare kafin aka sake Ajaero mintuna kafin wa'adin ya cika.
2. Omoyele Sowore
Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta kama tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya, Omoyele Sowore.
An ce jami'an DSS sun cafke Sowore lokacin da ya duro kasar a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagas.
Rahotanni sun ce kama Sowore ba zai rasa nasaba da kiran da ya yi na 'yan kasar nan su gudanar da zanga zangar adawa da gwamnati ba.
3. Dr. Abubakar Alkali
Wani lauya a Abuja, Deji Adeyanju ya tabbatar da cewa DSS ta cafke wani malami a Jami'ar Abuja (Baze).
Adeyanju ya ce hukumar ta kama malamin ne kan zargin goyon bayan zanga-zangar da aka yi a farkon watan Agustan 2024.
Rahotanni sun tabbatar cewa daga bisani hukumar ta wuce da Dr. Alkali zuwa jihar Sokoto.
4. Mamaye ofishin SERAP
A makon da ya gabata ne hukumar DSS ta mamaye ofishin SERAP bayan yi mata barazana kan karin farashin man fetur.
SERAP ta ce jami'an sun bukaci ganawa da daraktocinta bayan mamaye ofishin nasu ba bisa ka'ida ba inda ta bukaci Bola Tinubu ya umarce su da su fice daga ofishin.
5. Cin zarafi a Kano
An yi ta yada faifan bidiyo inda aka gano jami'an hukumar DSS na cin zarafin wasu mutane a birnin Kano.
Abba Hikima ya ce jami'an sun harbi wani matashi tare da cin zarafin mata da kuma dattawa a unguwar Badawa.
Ana zargin jami'an sun dauki matakin ne domin hana kwatar unguwa bin kofar gidan wani mai gidansu.
Abba Bichi ya musanta satar kudin mahaifinsa
Kun ji cewa dan tsohon daraktan hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi ya ƙaryata jita-jitar cewa ya sace kudin mahaifinsa.
Abba Bichi ya ce an yi ta yada cewa ya saci $2m kuma ya tsere ya bar kasa inda ya ce babu kamshin gaskiya a labarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng