Awanni bayan Dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu Ya Kawo Ziyara Arewa, Bayanai Sun Fito

Awanni bayan Dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu Ya Kawo Ziyara Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Maiduguri domin jajantawa al'ummar jihar Borno bisa ibtila'in da ya afku
  • Gwamna Babagana Umaru Zulum da wasu manyan ƙusoshin jihar Borno suka tarbi shugaban ƙasar ranar Litinin, 16 ga watan Satumba
  • A makon jiya ne ruwa ya yi ambaliya zuwa cikin birnin Maiduguri, wanda ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi ma su dumbin yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin jajantawa al'umma bisa ibtila'in ambaliyar da ta afku.

Rahoto ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya ne a jiya Lahadi da daddare bayan kammala ziyarar aiki a ƙasashen UAE, China da Burtaniya.

Kara karanta wannan

NMA ta hango wata matsala bayan ambaliya a Maiduguri, ta ba da mafita

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu ya kai ziyara jihar Borno domin jajantawa mutane sakamakon ambaliyar da ta faru Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jirgin shugaban ƙasa ya sauka a filin rundunar sojin saman Najeriya da ke jihar Borno da misalin ƙarfe 3:20 na rana yau Litinin.

Gwamnatin Tinubu ta bada tallafin N3bn

A lokacin da lamarin ya afku, Bola Tinubi ya tura mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima domin duba halin da ake ciki kasancewar ba ya ƙasar.

Shettima ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu za ta ba jihar Borno gudummuwar N3bn domin tallafawa waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Idan ba ku manta ba ambaliyar ruwan ta mamaye kusan rabin birnin maiduguri, lamarin da ya tilastawa dubban mutane barin gidajensu domin tsira.

Gwamnatin jihar Borno ta buɗe sansanonin ƴan gudun hijira 36 zuwa yanzu domin samarwa waɗanda suka rasa matsugunansu wurin da za su fake.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Atiku ya ziyarci Maiduguri, ya ba da gagarumar gudunmawa

Bola Tinubu ya dura Maiduguri

Gwamma Babagana Umaru Zulum da wasu ƙusoshin gwamnatin Borno ne suka tarbi shugaban ƙasar a lokacin da jirginsa ya sauka a Maiduguri, rahoton Punch.

Tinubu zai kai ziyarar ban girma ga Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar-Garbai El-Kaneni, sannan ana sa ran zai je daya daga cikin sansanoni domin yin jawabi ga ‘yan gudun hijira.

NMA ta hango ɓarkewar cututtuka a Maiduguri

A wani rahoton kuma Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta buƙaci gwamnatin Borno ta tashi tsaye ta ɗauki matakin kare lafiyar mutane bayan ambaliya.

Likitocin sun bayyana cewa akwai yiwuwar ɓarkewar cututtuka irinsu kwalara sakamakon cunkoson jama'a a sansanonin ƴan gudun hijira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262