NMA Ta Hango Wata Matsala bayan Ambaliya a Maiduguri, Ta Ba da Mafita

NMA Ta Hango Wata Matsala bayan Ambaliya a Maiduguri, Ta Ba da Mafita

  • Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta buƙaci gwamnatin jihar Borno ta tashi tsaye ta ɗauki matakin kare lafiyar mutane bayan ambaliya
  • Likitocin sun bayyana cewa akwai yiwuwar ɓarkewar cututtuka irinsu kwalara sakamakon cunkoson jama'a a sansanonin ƴan gudun hijira
  • NMA ta ce rashin ruwan sha mai tsafta da rashin tsaftar mahalli a sansanonin ƴan gudum hijira ka iya jawo cututtuka daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Maiduguri, Borno - Ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta ce da yiwuwar a samu ɓarkewar cututtuka a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kungiyar NMA ta yi wannan hasashen ne biyo bayan ambaliyar ruwan da ta afku a wasu sassan birnin a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Awanni bayan dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu ya kawo ziyara Arewa, bayanai sun fito

Taswirar jihar Borno.
NMA ta buƙaci gwammati ta ɗauki matakin daƙile ɓarkewar cututtuka bayan ambaliya a Maiduguri Hoto: Legit.ng
Asali: Original

NMA ta ba gwamnatin Borno shawara

A rahoton Daily Trust, NMA ta yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron lafiyar mutane a Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar likitocin reshen jihar Borno, Dr. El-Yakub Yakubu Mohammed ya fitar ranar Litinin.

Dokta El-Yaƙub ya kuma aike da saƙon jaje ga waɗanda ibtila'in ambaliyar ya rutsa da su, tare da ta'aziyyar waɗanda suka rasa rayukansu.

Ya jaddada bukatar tabbatar da tsaftar muhalli da sauran matakan da suka dace domin daƙile yiwuwar barkewar cututtuka kamar kwalara, Bussiness Day ta kawo.

Wasu irin cututtuka za su iya ɓarkewa a Maiduguri?

El-Yakub ya nuna damuwarsa kan rahotannin da aka samu daga sansanonin 'yan gudun hijira na cikin birnin Maiduguri cewa akwai yiwuwar wasu za su kamu da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Gwamna Zulum ya fadi babbar damuwarsa

"Kungiyar NMA reshen Borno na kira ga gwamnatin jiha ta gaggauta daukar matakin magance yiwuwar kamuwa da rashin lafiya sakamakon ambaliyar ruwa.
"Yayin da dubban mutane suka rasa matsugunansu, suka koma rayuwa cikin cunkoso da rashin samun ruwan sha mai tsafta da tsaftar muhalli, akwai yiwuwar barkewar cututtuka.
"Mutane na fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka kamar kwalara, zazzabin cizon sauro, da sauran cututtuka masu yaduwa a ruwa. Ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin kariya."

Shugaban NMA ya ƙara da cewa likitoci za su bada gudummuwa kana ya yi kira ga ɗaukacin ƴaƴan ƙungiyar su zauna cikin shirin domin kai ɗauki idan bukatar ta taso.

Maiduguri: Atiku ya bada gudummuwar N100m

A wani rahoton kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyarar jaje a jihar Borno sakamakon ambaliyar ruwa.

Atiku a yayin ziyarar ta sa ya ba da gudunmawar N100m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262