Jama'a Sun Razana bayan Jami'ai da Bindigu Sun Yi Awon Gaba da Kantoma a Kano
- Mazauna karamar hukumar Rimin Gado a Kano sun fada firgici bayan wasu jami'ai dauke da mugayen makamai sun kama cafke Kantoman
- Wani mazaunin yankin, Ahmad Rimin Gado ya bayyana wa Legit cewa da daddaren Asabar jami'an su ka shigo, hakan ya firgita jama'a
- Ya kara da cewa da farko, sun yi tunanin miyagun 'yan bindiga ne, amma daga baya aka tabbatar masu da cewa jami'an hukumar ICPC ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Mazauna unguwar Zango da ke karamar hukumar Rimin-gado a Kano sun shiga tashin hankali bayan wani al'amari da ya afku a garin.
Wasu mutane dauke da manyan bindigu ne su ka kutsa karamar hukumar a wani yanayi da ya sa jama'a fargabar ko masu garkuwa da mutane ne.
Ahmad Rimin Gado, mazaunin yankin ne kuma ya shaida wa Legit cewa jami'an sun yi awon gaba da shugaban riko na Karamar hukumar, Zangina Galadima Zango.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An gano wanda ya dauki Kantoma," Rimingado
Ahmad Rimingado ya kara da cewa bayan an dauke kantomansu ne su ka samu labarin cewa jami'an ICPC ne su ka yi awon gaba da shi.
Ya ce ba su taba wayar gari da irin wannan al'amari a Rimingado ba, lamarin da har yanzu ke kara sanya su cikin firgici.
Har yanzu kantoman Rimingado bai dawo ba
Wata majiyar ta bayyana cewa har yanzu ba a kai ga sanin inda shugaban riko na karamar hukumar Rimingado, Zangina Galadima Zango ya ke ba.
Lamarin na zuwa ne kwanaki kadan bayan jami'an tsaro sun cafke kantoman karamar hukumar Shanono, Malami Ibrahim Ashafa bisa zargin almundahana.
Ana binciken jamia'an gwamnatin Kano
A wani labarin, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta kasa (ICPC) ta fara binciken wasu jami'an majalisar dokokin jihar Kano bisa zargin tafka almundahana.
Daga cikin wadanda hukumar ta gayyata akwai kakakin majalisa Jibril Falgore, mataimakinsa Muhammad Butu da wasu mutane uku domin amsa tambayoyi kan N440m na sayen magani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng