A Karo na Biyu, Farashin Kayayyaki Ya Sauka a Najeriya, NBS Ta Fitar da Bayani
- Bayan sauƙin da aka samu a watan Yuli, hukumar NBS ta ce farashin kyayyaki ya sauka ko a watan Agastan 2024 da ta gabata.
- A alkaluman da hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar ranar Litinin, ta ce hauhawar farashi ya ragu da 1.25% a watan jiya
- Hukumar ta ce duk da haka a rahoton shekara-shekara, abinci ya ƙara tsada da 8.18% idan aka kwatanta da watan Agusta, 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a watan Agustan da ya gabata, 2024.
A bayanan da ta fitar yau Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024, hukumar NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu daga 33.40% a watan Yuli, zuwa 32.15% a watan Agusta.
The Nation ta rahoto cewa a wata takarda mai taken, "CPI Agusta 2024," NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu da kashi 1.25% a watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NBS: Yadda farashin kayayyaki suka sauka
Duk da tsadar rayuwar da ake ciki, NBS ta ce:
"Tashin farashin kayayyaki ya ƙara raguwa zuwa 32.15% a watan Agusta, 2024 idan aka kwatanta da 33.40%. na watan Yuli."
"Hakan na nufin hauhawar farashin ya ragu da kaso 1.25% a watan Agustan da ya shige idan aka kwatanta da farashin kayayyaki na watan Yuli, 2024."
A cewar hukumar NBS, duk da haka a alkaluman shekara-shekara, farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 6.35% sama da adadin da aka samu a watan Agustan 2023 (25.80%).
Kayan abinci sun ƙara tashi a Najeriya
NBS ta ce hauhawar farashin kayan abinci a watan Agustan 2024 ya kai kashi 37.52%, inda aka samu ƙarin kashi 8.18% idan aka kwatanta da watan Agustan 2023 (29.34%).
Ta ce an samu ƙarin hauhawar farashin kayan abinci ne sakamakon tsadar kayayyaki kamar burodi, masara, dawa, dankalin turawa, rogo, dabino, mai, kayan lambu, da sauransu.
NBS ta ce wasu kayan sun ƙara arha
A alƙaluman wata-wata kuwa hauhawar farashin abinci a watan Agustan 2024 ya tsaya a 2.37% wanda ya nuna raguwar 0.10% idan aka kwatanta da watan Yuli 2024 (2.47%).
NBS ta ce za a iya danganta hakan da faduwar farashin sigari, shayi, madara, Dankalin Turawa, doya, Rogo, kayan itatuwa da dai sauransu a cewar rahoton Channels tv.
Tsadar rayuwa: IMF ya ba Tinubu shawara
A wani rahoton kuma asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya bayyanawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu halin kuncin rayuwa da ake ciki a Najeriya
IMF ya tabbatar da cewa akwai buƙatar samar da hanyoyin da za su kawo sauki ga talakawa saboda halin da suke ciki a kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng