Gwamna Abba Ya ba da Tallafin N100m ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa a Maiduguri

Gwamna Abba Ya ba da Tallafin N100m ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa a Maiduguri

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kai tallafin Naira miliyan 100 ga al'ummar Maiduguri da ambaliyar ruwa ta rutsa da su
  • Gwamnatin Kano ta bayar da tallafin ne bayan da ta kai ziyarar duba irin barnar da ambaliyar ta yi tare da jajantawa al'ummar Borno
  • Gwamna Abba ya yi kira da a dauki matakin bai daya kan ambaliyar tare da ba jihar Borno tabbacin goyon bayan Kano a kowane lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Gwamnatin Kano ta mika tallafin ne ta hanyar takardar banki da ta ba gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ziyarar jaje da tawagarta ta kai Maiduguri.

Kara karanta wannan

"Ambaliyar Maiduguri za ta iya faruwa a Kano" APC ta fadi dalilin sa ido kan tallafin N3bn

Gwamna Abba Yusuf ya yi magana kan kaiwa 'yan Maioduguri daukin gaggawa
Gwamnatin Kano ta kai tallafin Naira miliyan 100 ga mutanen Maiduguri bayan ambaliya. Hoto: @HonAbdullahiM12
Asali: Twitter

Kano ta ba Borno tallafin N100m

Jaridar Leadership ta zayyana 'yan tawagar gwamnatin Kano da suka kai jajen da suka hada da Kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran 'yan tawagar sun hada da kwamishiniyar agaji da kawar da talauci Hajiya Amina Sani, da mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa da cigaban al'umma, Dakta Danyaro Yakasai.

An ce 'yan tawagar sun mika cekin Naira miliyan 100 ga Gwamna Zulum a madadin mai girma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

Abba ya jajantawa 'yan Maiduguri

Ta bakin 'yan tawagar, Gwamna Abba Yusuf ya jajanta wa wadanda ambaliyar ta shafa, inda ya bayyana ambaliyar a matsayin wani iftila'i mai sosa zuciya.

Ya yi kira da a hada kai domin tallafawa mutanen da abin ya shafa tare da jaddada goyon bayan Kano ga jihar Borno a wannan mawuyacin lokaci.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tallafin da za ta kaiwa mutanen Maiduguri

“Wannan iftila'i na bukatar daukar mataki na bai daya, kuma Kano na tare da jihar Borno a wannan mawuyacin hali da suke ciki.
Muna mika sakon ta'aziyyarmu ga wadanda suka rasa rayukansu, muna kuma yiwa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.”

- A cewar Gwamna Abba.

Gwamnati, Dangote sun kai tallafi Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan uku ga jihar Borno bayan ambaliyar ruwa a Maiduguri.

Hakazalika, na biyu a jerin masu kudin nahiyar Afrika, Aliko Dangote ya ba da tallafin Naira biliyan 1.5 domin a gudanar da ayyukan jin kai ga 'yan Maiduguri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.