Seaman Abbas: Muhimman Abubuwa 7 a Labarin Sojan Ruwan da Ya Ja Hankalin Ƴan Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Labarin abin da ya faru da wani sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna na ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin ƴan Najeriya a ƙarshen makon jiya.
Matar Abbas mai suna, Hussaina Iliyasu ta ba da labarin yadda aka azabtar da mijinta har sai da ya samu taɓin hankali saboda saɓanin da ya samu da mai gidansa.
Hussaina ta labarta dukkan abin da ta sani da kuma ƙoƙarin da ta yi wajen ganin an yi wa mijinta adalci a shirin Brekete Family, gidan rediyo da talabijin na ƴancin ɗan Adam.
Bidiyon da aka naɗa wanda ya karaɗe kafafem sada zumunta ya ja hankalin mutane, inda ƴan Najeriya suka fara sukar hukumar soji tare da neman a yi bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuni dai hedkwatar tsaro da ƙaraminin ministan tsaro, Bello Matawalle suka ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, sun ba da tabbacin za a yi adalci.
Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya kamata mu sani game da labarin Abbas.
1. Tafiya Sallah ba tare da izini ba
Asalin abin da ya faru a cewar Hussaina, Seaman Abbas Haruna ya bar filin faretin da aka tara su wajen karfe 6:00 na yamma a wata ranar Jumu'a domin zuwa Sallah.
Hussaina ta ce wannan zuwa Sallah da ya yi ba tare da neman izini ba, shi ne abin da ya ɓatawa kwamandan bataliyarsu M.S Adamu rai har ya nemi a ƙwace bindigarsa.
Lamarin dai ya faru ne bayan tura Abbas ya yi aiki a ƙarƙashin Birgediya Janar M. S Adamu a Sarti Baruwa da ke jihar Taraba.
2. Zargin Abbas da yunƙurin kisa
Bayan Abbas ya dawo daga masallacin, M. S Adamu ya nuna ɓacin ransa bisa tafiyar da ya yi ba tare da izini ba, ya umarci sojoji su karɓe bindigarsa.
Hussaina ta bayyana cewa a labarin da ta samu, mijinta ya yi turjiya saboda mutum ne mai ƙarfi kuma yana da jiki, kokawa ta ɓarke har dai bindiga ta tashi.
A cewarta, ɗaya daga cikin sojojin ya buga masa wani abu a kai, ya faɗi ƙasa, daga nan ogan ya laƙaba masa sharrin cewa zai kashe shi.
3. Dawo da Seaman Abbas Abuja
Hussaina ta ce ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin a kashe maganar tun kafin ta yi nisa amma abin ya ci tura sakamakon taurin kan M. S Adamu.
A bayananta ta ce abokan aikin Abbas sun ba ta shawarar ta je NDA Kaduna ta nemi alfarmar ogansu gaba ɗaya, Birgediya Umar Mu'azu domin ya sa baki a bar maganar.
Bayan kai komo da matar ta yi da kuma rashin hakurin M. S Adamu duk da ogansu ya sa baki, Hussaina ta ce an ci gaba da cin zarafin Abbas, daga baya aka dawo da shi Abuja.
4. Yadda Abbas ya samu tabin hankali
Raunin da aka ji masa a kai, tsare shi a ɗakin horo na gidan soja na daga cikin abubuwan da matar sojan ke zargin sun yi sanadin taɓuwar kwakwalwar mijinta.
Hussaina ta ce bayan dawo da Abbas Abuja, ta shirya tare da ƴaƴanta sun je ganinsa, amma suka taras da ya haukace kuma aka hana ta ɗauke shi zuwa asibiti.
Ta ce bayan kai-komo, Allah ya haɗa ta da wani soja wanda ya ba da izini aka kai mijinta asibiti sojoji na 44 kuma ya samu lafiya, amma sai aka maida shi aka tsare a Abuja.
5. Dangin Seaman Abbas
A ɓangaren ƴan uwan sojan ruwan, matarsa ta ce gaba ɗaya ba su damu da halin da yake ciki ba, mahaifiyarsa ce kaɗai ta taɓa zuwa Abuja ta gansa kuma ta koma.
A cewar Hussaina, lokacin da ƙuɗin hayar gidan da take zaune a Kaduna ya kare, ta koma Gombe wurin iyayensa, amma ta fuskanci kalubale da rashin kulawa.
Ta ce mijinta Abbas shi kaɗai ne Musulmi a danginsa, hakan ya sa ba su damu da halin da ya shiga ba, sai dai wata yayarsa guda ɗaya.
6. Shari'a a kotun sojoji
Bayan tsawon lokaci har Abbas ya fara komawa bakin aiki, M. S Adamu ya sake taso da batun, wanda ya kai ga fara shari'a a kotun sojoji.
Matar Seaman Abbas ta bayyana cewa ko an je kotun ba ya magana, sai idan ta zo ne yake buɗe baki ya yi magana.
Ta ce wani ɗan uwansa da ke aiki a NGO ne ya ɗauki lauyan da zai tsaya masa, to amma duk da haka ba ya magana saboda a ganinsa ana so ya amsa laifin da bai aikata ba.
7. Shekara 6 ana tsare da Abbas
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka tada hankalin mutane game da labarin Seaman Abbas shi ne yadda ya shafe shekaru kusan shida a cikin wannan hali.
Matar sojan ta ce tun 2018 aka fara binciken, kuma an azabtar da mijinta sosai wanda ya yi sanadin taɓuwar hankalinsa.
A halin yanzu gwamnatin Najeriya ta hannun ƙaraminin ministan tsaro, Bello Matawalle ta ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.
Dattawan Arewa sun yi Allah wadai
A wani rahoton kun ji cewa Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana takaicin labarin cin zarafin wani jami'in rundunar sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna
Jami'in hulda da jama'a a NEF, AbdulAzeez Suleiman ya ce yadda aka samu labarin Husaina Iliyasu kan cin zarafin mijinta ya jawo damuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng