"Ambaliyar Maiduguri za Ta Iya Faruwa a Kano" APC Ta Fadi Dalilin Sa Ido kan Tallafin N3bn

"Ambaliyar Maiduguri za Ta Iya Faruwa a Kano" APC Ta Fadi Dalilin Sa Ido kan Tallafin N3bn

  • APC a Kano ta bayyana cewa za ta sa ido a kan yadda za a yi amfani da tallafin ambaliya da gwamnatin Bola Tinubu ta ba Kano
  • Gwamnatin tarayya ta ba gwamnatin Abba Kabir Yusuf tallafin ambaliya har Naira Biliyan uku domin taimakon jama'ar jihar
  • A zantawarsa da Legit, sakataren yada labaran APC, Ahmed Aruwan ya ce dole su tabbatar an yi amfani da kudin ba tare da an wawashe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam’iyyar APC a Kano ta bayyana cewa za ta sa ido kan yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta yi amfani da tallafin gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ba da tallafin N100m ga wadanda ambaliya ta shafa a Maiduguri

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ba gwamnatin Abba Kabir Yusuf tallafin kudin ambaliya na Naira Biliyan Uku.

Ganduje
N3bn: APC za ta sa ido kan tallafin gwamnatin tarayya ga Kano Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar Lahadi ne shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya ce za su tabbatar an kashe kudin bisa ka’ida ta hanyar bibiya da sa ido.

"Akwai dalilin sa ido kan tallafin:" APC

A karin bayanin da ya yi wa Legit, sakataren yada labaran APC na Kano, Ahmed S Aruwan ya zargi gwamnatin NNPP da lamushe tallafin da aka bayar a baya.

Ya kara da cewa iftila’in da ya afku a jihar Borno inda mutane da dama su ka rasa rayukansu a mummunan ambaliya zai iya afkuwa a Kano.

Yadda tallafin Tinubu zai amfani Kano

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa idan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi amfani da tallafin da gwamatin tarayya ta bayar, jama'a za su samu sauki.

Kara karanta wannan

"Da mu muke mulki, ba za a janye tallafin fetur kamar yadda Tinubu ya yi ba," inji shugaban PDP

Ahmed S Aruwan ya kara cewa kamar Maiduguri, akwai madatsun ruwa a Kano, saboda haka za su sa ido domin ganin an yi amfani da kudin wajen kare afkuwar mummunar ambaliya.

Kano: Shugaban APC ya kaddamar da tallafi

A baya kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya raba tallafi ga matasa mata da maza a jihar guda 484 a wani yunkuri na rage masu radadin rayuwa.

Dr. Ganduje ya bayyana cewa an raba tallafin ne domin mutunta umarnin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan masu rike da makaman gwamnati da su tallafa wa jama'ar kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.