Yan Bindiga Sun Harbe Su, Sun Wulakanta Gawar duk da Karɓar Miliyoyin Kudin Fansa
- Yan bindiga da suka kama wani mai otel da matarsa da wasu manyan ma'aikatan na otel sun harbe su har lahira
- Rahotanni sun nuna bayan harbe mutanen, yan bindigar sun yi watsi da gawarsu kafin a samo su a cikin wani daji
- Haka zalika yan bindigar sun karbi kudin fansa kafin kashe mutanen kuma sun harbe wadanda suka kai musu kuɗin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Yan bindiga sun harbe wani mai otel da ma'aikatan otel din a jihar Neja a Arewa ta tsakiyar Najeriya.
Rahotonni sun nuna cewa yan bindiga sun kama mutanen ne a kauyen Gauraka a karamar hukumar Tafa a jihar Neja.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa yan bindigar sun karbi kudin fansa har N25m kafin su hallaka mutanen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda 'yan bindiga suka kama mutanen
A ranar 17 ga watan Agusta ne yan bindiga suka afka kan mutane a cikin wani hotel a Gauraka da ke Tafa.
Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa yan bindigar sun kai hari otel din ne da misalin karfe 1:00 na dare inda suka tafi da dukkan mutanen da suke nan.
Miyagun 'yan bindiga sun harbe mutanen
Bayan garkuwa da mutanen, yan bindigar sun bukaci kudin fansa N25m amma sai suka kashe wadanda suka kai musu kuɗin.
Bayan haka sun harbe mai otel din, manajansa da wani mutum da ya je kwana a cikin yayin da suka kai harin.
Bayan sun harbe mutanen a Dogon-Daji sai suka watsar da gawarsu kafin a same su a a yi musu janaza a ranar Lahadi.
An ceto mutum a hannun yan bindiga
Jagoran yan banga a Tafa, Hussaini Abubakar ya bayyana cewa an ceto wani mutum daya da yan bindigar suka sace bayan an yi musayar wuta.
Hussaini Abubakar ya ce wanda aka ceton ya samu raunuka kuma a yanzu haka yana asibitin sojoji domin karɓar magani.
Yan bindiga sun harbe dan kasuwa
A wani rahoton, mun ji cewa yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Enugu a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Enugu ta Kudu.
Miyagun ƴan bindigar sun hallaka shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar Ogbete bayan sun binidige shi har lahira yayin harin da suka kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng