Hatsarin Jirgi: Gwamnan Zamfara Ya Kadu kan Asarar Rayukan Mutum 40, Ya Ba da Umarni

Hatsarin Jirgi: Gwamnan Zamfara Ya Kadu kan Asarar Rayukan Mutum 40, Ya Ba da Umarni

  • Gwamnan jihar Zamfara ya nuna alhininsa kan hatsarin jirgin ruwan da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 40
  • Dauda Lawal ya bayyana hatsarin da ya auku a rafin Bakin Kasuwa da ke ƙaramar hukumar Gummi a matsayi babban bala'i
  • Gwamna Dauda ya umarci hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ta gaggauta kai ɗauki domin ciro gawarwakin mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaɗu kan mutuwar mutane sama da 40 sakamakon hatsarin jirgin ruwa.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a rafin Bakin Kasuwa na ƙauyen Uban Dawaki da ke ƙaramar hukumar Gummi a matsayin babban bala’i.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Kalamam gwamnan PDP sun tayar da kura ana dab da fara zabe

Dauda Lawal ya kadu kan hatsarin jirgin ruwa a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal ya yi alhinin rasuwar mutane a hatsarin jirgin ruwa na Zamfara Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

Mutanen sun rasu ne a lokacin da jirgin ruwan da ke ɗauke da mutane sama da 50 ya kife a rafin na Bakin Kasuwa.

Me gwamnan Zamfara ya ce kan hatsarin?

Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Idris ya fitar a shafinsa na Facebook.

Sulaiman Idris, a cikin sanarwar ya ambato Gwamna Dauda yana bayyana lamarin a matsayin babban bala’i.

"Mun samu rahoton wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a rafin Bakin Kasuwa da ke ƙauyen Uban Dawaki a ƙaramar hukumar Gummi, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka sama da 40."
"Gwamna ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jiha (SEMA) da ta fara kai ɗauki cikin gaggawa tare da ciro gawarwakin mutanen."

Kara karanta wannan

An rasa rayuka yayin da jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya kife a jihar Arewa

- Sulaiman Bala Idris

"Gwamnan ya kuma umurci hukumar da ta ɗauki matakin gaggawa domin tantance girman hatsarin tare da bayar da agajin gaggawa."

Gwamna Dauda ya umarci a ba da tallafi

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya kuma umurci kwamishinan jin ƙai da ba da agaji na jihar da ya kai kayan agaji cikin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa da iyalansu.

Gwamna Dauda Lawal ya kuma yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda lamarin ya ritsa da su, tare da ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen hana aukuwar hakan a nan gaba.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a kogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da bacewar wasu 15 a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a kogin Gamoda da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.

Hatsarin ya auku ne a kauyen Nahuce a ranar Alhamis lokacin da fasinjojin jirgin ke kokarin tsallaka kogin bayan dawowa daga kasuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng