Mauludin Nabiyyi: Gwamnan Jigawa Ya Kara Ranar Hutu ga Ma'aikata

Mauludin Nabiyyi: Gwamnan Jigawa Ya Kara Ranar Hutu ga Ma'aikata

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta ƙara ranar da ma'aikata za su yi hutu saboda murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW)
  • Gwamnatin ta ayyana ranar Talata, 17 ga watan Satumban 2024 a matsayin ranar da ma'aikata ba za su je aiki ba a jihar Jigawa
  • Ta yi kira a gare su da su yi amfani da lokacin wajen yi wa shugabanni addu'o'i domin samun kariya da yin jagoranci mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana ranar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta ayyana ranar Talata 17 ga Satumba, 2024 a matsayin ranar hutu.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Atiku ya ziyarci Maiduguri, ya ba da gagarumar gudunmawa

Gwamnatin Jigawa ta ba da hutu
Gwamnatin Jigawa ta kara ranar hutu saboda Mauludin Annabi SAW Hoto: @aunamadi
Asali: Twitter

Za a yi hutun Mauludi a jihar Jigawa

Jaridar Leadership ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Jigawa, Muhammad K. Dagaceri.

Sanarwar ta fito ne ta hannun kakakin Muhammad K. Dagaceri, Kwamared Samaila Ibrahim Dutse.

Ku tuna cewa a ranar Juma’a 13 ga watan Satumba, 2024 gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 16 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW).

Gwamnatin Jigawa ta ba da hutun Mauludi

"Ina sanar da cewa gwamnati ta ayyana ranar 14 ga watan R/Awwal, 1446AH (17 ga watan Satumba 2024) a matsayin ranar da babu aiki domin murnar Mauludin Annabi Muhammad (S.A.W)."
"Gwamnatin jihar Jigawa na taya ɗaukacin al’ummar musulmin jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya murnar zagayowar bikin na wannan shekarar."

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya kinkimo aikin N340m a jami'ar UMYUK

"Muna fatan za a yi amfani da shi wajen tunani da kuma ƙarfafa yin riƙo da koyarwa da kyawawan ɗabi’un Manzon Allah (SAW)."

- Muhammad K. Dageceri

Muhammad Dagaceri, ya yi kira ga ma’aikatan jihar da su yi amfani da lokacin wajen roƙon Allah (S.W.A) ya ba shugabanninsu kariya da yi musu jagora domin samun zaman lafiya da ci gaba a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan Jigawa ya ba da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.

Gwamna Namadi ya amince da fitar da N315.5m ga mutane 15,775 da suke a sansanonin ƴan gudun hijira a cikin ƙananan hukumomi 20 da ambaliyar ta shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng