Hotuna: Fursunoni 274 Sun Tsere daga Gidan Yarin Maiduguri bayan Ambaliyar Ruwa
- Hukumar kula da gidan yarin Najeriya (NCoS) ta bayyana cewa fursunoni 274 ne suka tsere bayan ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri
- Hukumar ta ce fursunonin sun tsere ne lokacin da ake kwashe su daga matsakaiciyar cibiyar tsaro ta Maiduguri bayan rushewar katangarta
- Sai dai hukumar ta ba da tabbacin cewa tana adane da bayanan fursunonin harma da shacin yatsunsu kuma za a kamo su nan ba da jimawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Hukumar da ke kula da gidajen yarin Najeriya ta ce fursunoni 281 sun tsere daga matsakaiciyar cibiyar tsare masu laifi da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Hukumar ta bayyana cewa fursunonin sun tsere a lokacin da ake kwashe su daga gidan cibiyar tsaron bayan afkuwar ambaliyar ruwa a jihar.
Ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri
Kakakin hukumar NCoS, Umar Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a Abuja, ranar Lahadi kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ambaliyar ruwan da ta mamaye sassa daban-daban na Maiduguri ta shafi mutane sama da miliyan guda, tare da haddasa mutuwar mutane akalla 30.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta dukufa wajen gudanar da ayyukan ceto, inda ta ceci mutane sama da 400 da ambaliyar ruwa ta rutsa da su.
Fursunoni 274 sun tsere a Maiduguri
Umar Abubakar ya ce hukumar ta adana bayanan fursunonin da suka tseere tare da shacin yatsunsu.
The Punch ta rahoto Mista Umar ya ce:
“Ambaliyar ta rusa katangar gidan gyaran halin, ciki har da matsakaiciyar cibiyar tsaro ta Maiduguri (MSCC) da gidajen ma’aikata da ke cikin birnin.
“Bayan jami’an hukumar NCoS tare da goyon bayan wasu hukumomin tsaro sun kwashe fursunonin zuwa wani wuri mai tsaro na daban, an gano fursunoni 281 sun tsere.
“Yanzu haka, san sake cafko jimillar fursunoni bakwai kuma an mayar da su gidan yarin, yayin da ake kokarin nemo sauran domin mayar da su inda suke a tsare."
Fursunoni sun tsere a Suleja
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta bayyana cewa fursunoni 69 suka tsere daga gidan gyaran hali na Suleja a jihar Neja.
Hukumar kula da gidajen yarin ta ce ta zabi bayyana bayanan fursunonin ne domin ganin an kamo su tare da mayar da su gidan yarin cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng