Halilu Buzu: Bulama Bukarti Ya Kafa Asusun Tallafi ga Sojoji, Sun ba da N1.8m

Halilu Buzu: Bulama Bukarti Ya Kafa Asusun Tallafi ga Sojoji, Sun ba da N1.8m

  • Yayin da aka ba sojoji kyautar kudi bayan kisan Halilu Sabubu, wasu yan Najeriya sun kaddamar da asusun tallafa musu
  • Lauya Bulama Bukarti da abokansa sun shirya hakan ne domin nunawa sojojin yan Najeriya suna tare da su a kowane lokaci
  • Wannan na zuwa ne bayan kisan Halilu Sabubu da sojoji suka yi da safiyar ranar Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Fitaccen lauya, Bulama Bukarti ya kaddamar da wani asusu na musamman ga sojojin da suka hallaka Halilu Sabubu.

Bukarti ya ce sun dauki wannan mataki ne domin nuna goyon baya ga dakarun sojoji da ke yakar yan bindiga.

Bulama Bukarti ya kafa asusun tallafawa sojojin da suka hallaka Sabubu
Bayan kisan Halilu Sabubu, Bulama Bukarti ya kafa asusun tallafawa sojoji. Hoto: Audu Bulama Bukarti.
Asali: Facebook

Halilu Sabubu: Bulama Bukarti sun tallafawa sojoji

Kara karanta wannan

Halilu Sabubu: Malamin Musulunci ya shawarci Bello Turji da sauran miyagu

Lauyan ya bayyana haka ne a yau Lahadi 15 ga watan Satumar 2024 a shafinsa na X domin tallafawa sojojin.

Bukarti ya ce abin takaici ne yadda sojoji ke sadaukar da rayuwarsu a fagen daga amma abin da ake biyansu bai taka kara ya karya ba.

Ya ce sojoji 26 ne suka yi nasarar hallaka Halilu Sabubu amma kyautar da aka yi musu bai kai sadaukarwar da suka yi ba.

"Ba za mu jira gwamnati ta yi wani abu ba, a matsayinmu na yan Najeriya dole mu yi wani abu, kungiyarmu ta Fashin Baki a Facebook duk mako da kara N1.8m ga sojojin."
"Sannan muna kaddamar asusu na musamman domin iyalansu su samu abin da ya kamace su, wannan dama ce da za mu nuna muna mutunta sadaukarwarsu."

Kara karanta wannan

Bayan shekaru, Gwamna Abba ya sakawa yarinyar da taimaka masa a zaben 2019

"Muna kiran yan Najeriya masu sha'awar taimakawa da su tuntubi Jaafar Jaafar ko ni kai tsaye, ya kamata mu nunawa sojojinmu muna tare da su yayin da wasu yan siyasa ba su damu ba."
Bulama Bukarti

Bulama ya koka kan yadda ake biyan sojojin albashi duk da sadaukar da rayuwarsu da suke yi a yaki da ta'addanci.

Bulama Bukarti ya magantu kan bidiyon Turji

Kun ji cewa bayan sabon bidiyo da Bello Turji ya yi yana gargadin Audu Bulama Bukarti, lauyan ya yi martani ga dan ta'addan a makon jiya.

Bukarti ya kalubalanci Turji inda ya ce a baya shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi masa barazana irin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.