Gobara Ta Lakume Kasuwar Katako Kurmus, an Fadi Asarar da Aka Yi
- Mutane da dama sun tafka asara bayan gobara ta tashi a kasuwar katako ta Itamaga a Ikorodu da ke jihar Lagos
- Daraktan hukumar ba da agajin gaggawa, Nosa Okunbor ya ce gobarar ta jawo mummunan asara na miliyoyi a jihar
- Okunbor ya ce an tabbatar da cewa matsalar wutar lantarki ne ya jawo gobarar kafin nasarar dakile ta cikin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An shiga wani irin yanayi bayan gobara ta kama a wata kasuwar katako da ke jihar Lagos.
Gobarar ta kama ne da safiya a kasuwar Itamaga da ke Ikorodu wanda ya yi sanadin asarar miliyoyi.
Gobara ta lakume kasuwar katako a Lagos
Daraktan hukumar ba da agajin gaggawa a jihar, Nosa Okunbor shi ya tabbatar da haka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Okunbor ya ce gobarar ta fara da misalin karfe 3.00 na dare wanda ta yi sanadin lakume shaguna makare da dukiyoyi.
Yayin da masu ba da taimakon gaggawa suka zo, Okunbor ya ce sun gano cewa gobarar ta kama ne saboda matsalar wutar lantarki.
Ya ce zuwan masu ba da agajin da kuma jami'an hukumar kashe gobara ya yi tasiri wurin dakile matsalar, cewar rahoton Tribune.
An gano musabbabin gobarar a Lagos
"Bayan zuwan masu ba da agaji, an gano wutar lantarki ta jawo gobarar da ta lakume shaguna da dama."
"An gudanar da bincike mai zurfi inda aka gano cewa matsalar wutar lantarki ne daga wani bangare ya jawo."
"Gudunmawar da hukumomi da hukumar kashe gobara ta jihar Lagos sun tabbatar da kawo karshen gobarar."
Nosa Okunbor
Jarumin fina finai ya kwanta dama
Kun ji cewa masana'antar shirya fina-finan Nollywood a Najeriya ta shiga jimami bayan rasuwar jarumi, Shina Sanyaolu a jihar Lagos.
Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba 11 ga watan Satumbar 2024 duk da ba a bayyana silar mutuwar jarumin ba.
Jaruman fina-finan Nollywood da dama sun tura sakon ta'aziyya inda suka tabbatar da cewa Shina mutumin kirki ne.
Asali: Legit.ng