Gwamna Radda Ya Kinkimo Aikin N340m a Jami'ar UMYUK

Gwamna Radda Ya Kinkimo Aikin N340m a Jami'ar UMYUK

  • Gwamnan jihar Katsina ya nuna damuwarsa kan rahoton da ya samu dangane da lalacewar wutar lantarki a jami'ar UMYUK
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince a fitar da N340m domin gyara wutar lantarkin wacce ta lalace a jami'ar
  • Gwamnatin ta ɗauki matakin yin gyaran ne da nufin magance matsalar ɓarnata kayayyaki da rashin tsaro a jami'ar UMYUK da ke Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya amince da fitar da Naira miliyan 340 domin yin wani aiki a jami'ar Umaru Musa Yar'adua (UMYUK) da ke Katsina.

Gwamna Radda ya amince a fitar da kuɗin ne domin gyara wutar lantarki a jami’ar UMYUK wacce ke cikin birnin Katsina.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan babban dan majalisar PDP ya riga mu gidan gaskiya

Gwamna Radda zai yi aiki a jami'ar UMYUK
Gwamna Radda ya amince a gyara wutar lantarkin jami'ar UMYUK Hoto: Dr Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa ta hannun daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Abdullahi Aliyu-Yar’adua, cewar rahoton jaridar Tribune.

Radda ya amince a yi gyara a UMYUƘ

Alhaji Aliyu Yar’adua ya ce gwamnan ya amince da gaggauta fitar da kuɗin domin gudanar da ayyuka guda biyu kan wutar lantarki a jami’ar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Gwamna Radda ya nuna damuwa kan rahoton rashin wutar lantarki da ya addabi jami’ar, hakan ya sanya ya ba da umarnin gyarawa nan take."
"Da farko dai, za a sauya na’ura mai ƙarfin 33KVA da wasu na’urorin da suke ba jami'ar lantarki a kan kuɗi sama da Naira miliyan 260, da kuma sanya fitulun tsaro masu amfani da hasken rana wanda aka bayar kan kuɗi sama da Naira miliyan 98."

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

Alhaji Aliyu Yar'adua

A cewar Alhaji Aliyu Yar’adua, matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na nufin magance matsalar ɓarnata kayayyaki da rashin tsaro a jami’ar.

Gwamna Radda ya yi abin a yaba

Legit Hausa ta tuntuɓi wani ɗalibi da ke karatu a jami'ar UMYUK mai suna Iliyasu Abubakar wanda ya yaba da wannan matakin da gwamnan ya ɗauka.

"Tabbas wannan abin a yaba ne indai har za a yi aikin domin mun daɗe muna shan wuya sakamakon rashin wutar lantarki. Amma tun da yanzu an ce an fitar da kuɗin muna fatan za a yi aikin gyaran."

- Iliyasu Abubakar

Gwamna Radda ya magantu kan biyan N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamna Dikko Radda ta yi alkawarin ne yayin da yake magana kan jin ra'ayin al'umma a kan kasafin kudin shekarar 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng