An Rasa Rayuka yayin da Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji Ya Kife a Jihar Arewa

An Rasa Rayuka yayin da Jirgin Ruwa Dauke da Fasinjoji Ya Kife a Jihar Arewa

  • Wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar rasuwar mutane masu tarin yawa
  • Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane sama da 40 ne suka rasu sakamakon hatsarin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Gummi
  • Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ya bayyana cewa jirgin ruwan na ɗauke fasinjoji sama da 50 ne lokacin da hatsarin ya auku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya gamu da hatsari a jihar Zamfara.

Aƙalla mutane 41 da suka haɗa da mata da yara suka rasu bayan jirgin ruwan mai ɗauke da fasinjoji 53 ya kife a garin Gummi, ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ambaliyar ruwa, gini ya rufto kan daliban jami'a

Jirgin ruwa ya kife a Zamfara
Fasinjoji sun rasu yayin jirgin ruwa ya kife a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda hatsarin jirgin ya auku

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hatsarin jirgin ruwan ya auku ne a ranar Asabar, 14 ga watan Satumban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin garin Gummi mai suna, Safiyanu Dan Iya, ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne lokacin da jirgin wanda aka ɗorawa kaya masu yawa ya haɗe da wani wanda babu komai a cikinsa a rafin Mashayar Yan Tauri.

Safiyanu Dan Iya ya yi bayanin cewa matuƙin jirgin da babu komai a ciki yana ƙoƙarin rage fasinjojin da ke cikin ɗayan jirgin ne lokacin da kwatsam suka yi karo wanda hakan ya sa jirgin mai ɗauke fasinjoji ya kife tare da nutsewa a rafin.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa jirgin yana ɗauke ne da mutane 53 inda aka ceto mutum 12 ciki har da direban yayin da sauran mutum 41 suka rasu.

Kara karanta wannan

Kasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya turo saƙo kan harajin N50m da ya sa a Zamfara

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Zamfara (ZEMA), Hassan Dauran ya shaidawa Channels tv cewa jirgin na ɗauke da mutane sama da 50 lokacin da lamarin ya auku.

Ya bayyana cewa ƴan kaɗan daga cikinsu kawai aka samu nasarar cetowa yayin da sauran ba su tsira da ransu ba.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Jigawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutane biyar sun rasa rayukansu yayin da wani Kwae-kwale ya kife a garin Ganta da ke karamar hukumar Buji a jihar Jigawa.

Kwale-kwalen wanda ya ɗauko fasinjoji da dama ya gamu da haɗari ne a yammacin ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng