Halilu Sabubu: Malamin Musulunci Ya Shawarci Bello Turji da Sauran Miyagu

Halilu Sabubu: Malamin Musulunci Ya Shawarci Bello Turji da Sauran Miyagu

  • Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya tura sako na musamman ga Bello Turji da sauran yan ta'adda bayan kisan Halilu Sabubu
  • Malamin ya bukaci yan ta'addan da su tuba su dawo hanyar Allah duba da yadda ake kashe su inda ya ce su mutuwa a layin da suke ba kyau
  • Sheikh Assadus Sunna ya yabawa jami'an tsaro kan irin wannan kokari da suka yi inda ya ce sun cancanci yabo na musamman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Malamin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yabawa jami'an tsaro kan yaki da ta'addanci.

Shehin malamin ya shawarci Bello Turji da sauran yan ta'adda da su ajiye makamansu duba da yadda ake kashe su.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta gwangwaje dakarun da suka hallaka dan ta'adda, Halilu Sabubu

Malamin Musulunci ya tura sako ga Bello Turji bayan kisan Sabubu
Sheikh Musa Assadus Sunnah ya shawarci Bello Turji da sauran yan bindiga su ajiye makamansu. Hoto: Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah, @ZagazOlamakama.
Asali: Facebook

Sabubu: Sheikh Assadus Sunnah ya shawarci Turji

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren jiya Asabar 14 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Musa Yusuf ya shawarci al'umma da su kasance masu uzuri da kuma zaton alheri musamman game da jami'an tsaro a kasar.

Ya koka kan yadda mutane suka yi ta sukarsu bayan tarewarsu a jihar Sokoto da cewa wasan kwaikwayo ne kawai.

Assadus Sunnah ya ja kunnen Bello Turji

"Mutum nawa ne suka bar duniya ta wannar hanya, kafin Halilu Sabubu da ya mutu kwanan nan, a bidiyon da ya yi shi kansa idan aka ce zai mutu watakila ba zai yarda ba."
"Kafin shi an kashe Kacalla Ari da Damina da ire-irensu duk a wannar hanya sun mutu duk da irin makaman da suke da shi."

Kara karanta wannan

Bidiyon Halilu Sabubu na karshe da yake rokon Bello Turji, ya tura sako ga malamai

"A sakon Sabubu a bidiyo ya fada cewa ku ragawa yan uwanku Fulani, ashe akwai yan uwanku Fulani da ba su aminta da cutarwarku ba."
"Muna kira ga dukkan yan bindiga da wadanda suka dauki sata sana'a ya kamaya ku ji tsoron Allah ku ajiye makamnku domin al'umma ta zauna lafiya."

- Sheikh Yusuf Assadus Sunnah

Bidiyon Sabubu na karhse kafin hallaka shi

Kun ji cewa an wallafa faifan bidiyo inda marigayi dan ta'adda, Halilu Sabubu ya ke rokon yan uwansa kan lamarin tsaro.

Sabubu ya kira manyan yan bindiga da suka hada da Bello Turji da Alhaji Ado da Alhaji Shingi domin kawo karshen lamarin.

Sabubu ya wallafa bidiyon ne a ranar Talata 10 ga watan Satumbar 2024 kwanaki uku kafin sojoji su hallaka shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.