An Shiga Jimami bayan Babban Dan Majalisar PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami bayan Babban Dan Majalisar PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Majalisar dokokin jihar Neja ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta wanda ya mutu bayan ya yi ƴar gajeruwar jinya
  • Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na majalisar, Malam Farouq Isah ne ya sanar da mutuwar Mista Joseph Duza a birnin Minna
  • Kafin mutuwar ɗan majalisar na jam'iyyar PDP wanda ke wakiltar ƙaramar hukumar Munya, shi ne shugaban kwamitin tsaro da leƙen asiri na majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Majalisar dokokin jihar Neja ta yi rashin ɗaya daga cikin mambobinta.

Majalisar dokokin ta sanar da mutuwar Mista Joseph Duza mai wakiltar ƙaramar hukumar Munya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Dan majalisar Neja ya rasu
Dan majalisar dokokin jihar Neja ya rasu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ɗan majalisar PDP ya rasu a Neja

Jaridar The Nation ta rahoto cewa daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na majalisar, Malam Farouq Isah, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 13 ga watan Satumban 2024.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ambaliyar ruwa, gini ya rufto kan daliban jami'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Farouq Isah ya sanar da mutuwar ɗan majalisar ne a birnin Minna, babban birnin jihar Neja, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Kafin mutuwarsa, Misata Joseph Duza shi ne shugaban kwamitin majalisar kan tsaro da leƙen asiri.

Malam Farouq Isah ya bayyana cewa ɗan majalisar ya yi bankwana da duniya ne bayan ya yi gajeruwar rashin lafiya sannan ya yi addu'ar Allah ya jiƙan ɗan majalisar.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya ba shugabannin majalisar, mambobi, ma'aikatan majalisar da mutanen Munya haƙuri da juriyar wannan rashin da aka yi.

Karanta wasu.labaran kan jihar Neja

Tsohon ɗan majalisa ya rasu

Kara karanta wannan

Kasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya turo saƙo kan harajin N50m da ya sa a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan majalisar wakilai daga jijar Legas, Wole Diya ya rasu a ranar Juma'a 9 ga watan Agustan 2024 yana da shekaru 63 a duniya.

Tsohon ɗan majalisar wanda ya wakilci mazaɓar Somolu a majalisar wakilai har sau biyu ya ya rasa ransa kwanaki kadan kafin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng