Daga Karshe Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Lokacin Fara Jigilar Fetur daga Matatar Dangote

Daga Karshe Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Lokacin Fara Jigilar Fetur daga Matatar Dangote

  • Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan lokacin da za a fara jigilar man fetur daga matatar man Dangote da ke Legas
  • Ministan kuɗi ya bayyana cewa daga ranar Lahadi, 15 ha watan Satumban 2024 za a fara jigilar man fetur daga matatar ta Dangote
  • Sai dai, ministan ya ƙara da cewa a yanzu kamfanin NNPCL kaɗai za a ba man fetur wanda shi ne zai riƙa rabawa ƴan kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin da za a fara fitar da man fetur daga matatar Dangote.

Gwamnatin ta hannun ministan kuɗi, Wale Edun, ya ce matatar Dangote za ta fara raba man fetur daga ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki bayan fara raɗe raɗin ya rasu

Dangote zai fara fitar da fetur
Matatar Dangote za ta fara fitar da fetur ranar Lahadi Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Wale Edun ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma'a, 13 ga watan Satumban 2024.

Dangote zai ba NNPCL fetur

Ministan wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS), Dr Zacch Adedeji, ya kuma ce kamfanin NNPCL kawai matatar za ta riƙa ba man fetur, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

"Ina farin cikin sanar da cewa an kammala dukkanin yarjejeniyoyin kuma za a fara lodin kashin farko na man fetur daga matatar Dangote a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba."
"Daga ranar 1 ga watan Oktoba, kamfanin NNPCL zai fara samar da kusan ganga dubu 385 ta ɗanyen mai a kullum ga matatar Dangote, wanda za a biya a Naira."
"Hakaazalika, matatar Dangote za ta samar da man fetur da dizal ga kasuwannin cikin gida, wanda za a biya a Naira."

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun gama karaya da matatar Dangote, sun fadi sharadin sayen fetur

"Matatar Dangote za ta siyar da dizal a Naira ga duk ɗan kasuwan da ke so. A yanzu NNPCL kaɗai za a sayarwa man fetur, daga nan NNPCL zai sayarwa ƴan kasuwa daban-daban."

- Zacch Adedeji

NNPCL ya magantu kan farashin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya yi magana kan raguwar farashin man fetur sakamakon fara aikin matatar Dangote.

Kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa cewa fara jigilar man fetur daga matatar Dangote ba shi ba ne yake nuna za a samun raguwar farashin man fetur ɗin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng