"Jira Ya Ƙare": Gwamnatin Tinubu Ta Yi Maganar Tsarin Biyan Sabon Albashi na N70,000

"Jira Ya Ƙare": Gwamnatin Tinubu Ta Yi Maganar Tsarin Biyan Sabon Albashi na N70,000

  • Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da daɗewa ba za a kammala tsara samfurin da za a bi wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi
  • Ƙaramar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Nkeruka Onyejeocha ce ta bayyana haka a wurin taro a Abuja ranar Jumu'a
  • Ministar ta ce kwamitin da aka kafa wanda ya kunshi wakilan gwamnati, ƴan kwadago da kamfanoni na ci gaba da aiki kan batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Karamar ministar ƙwadago da samar da aikin yi, Nkeruka Onyejeocha, ta ba da tabbacin cewa za a fitar da taswirar sabon mafi karancin albashi nan ba da daɗewa ba.

Ministar ta tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta fitar tsarin da za a bi wajen aiwatar da sabon albashin da zarar an kammala.

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta yi wa ma'aikata albishin kan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Ta bayyana hakan ne ranar Juma’a a wurin wani taro da ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta shirya a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ina aka kwana kan batun ƙarin albashi?

Nkeruka Onyejeocha ta yi bayanin cewa kwamitin da aka kafa wanda ya kunshi wakilan ƴan kwadago, kamfanoni masu zaman kansu da gwamnati za su zauna kan batun.

A cewarta, kwamitin zai zauna da shugabar ma'aikatar gwamnatin tarayya domin tsara samfuri da tawirar yadda ƙarin albashin zai kasance, rahoton Punch.

Ministar ta ƙara da cewa bai kamata a ɗora laifin jinkirin da aka samu wajen fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin kan gwamnatin tarayya ba saboda ita ma NLC tana da laifi.

Onyejeocha ta ce a halin yanzu gwamnati da kwamitin sabon albashin na ci gaba da zaman tattaunawa domin ƙarƙare komai kuma za su gama nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Sabon albashi: Gwamnan Kano ya fadi lokacin da zai fara biyan ma'aikata N70000

Yaushe gwamnatin Tinubu za ta fara biyan N70,000?

Ƙaramar ministar ta ce:

"Yanzu da nake magana da ku ɓangaren gwamnati na gudanar da taro kan batun, kuma da ƙarfe 2:00 na rana kwamitin zai gana da shugabar ma'aikata."
"Da zaran sun ƙarƙare nawa ya kamata a riƙa biyan kowane ma'aikaci, za mu fara biya ba tare da ɓata lokaci ba."

Wani ma'aikacin gwamnati a Katsina, Haruna Bashir ya shaidawa Legit Hausa cewa sun gaji da gafara sa amma ba su ga ƙaho ba.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta nuna ba ta damu da halin da ƴan ƙasa musamman ma'aikata suka shiga ba.

Haruna ya ce:

"Idan ka duba duk gwamnan da ya yi magana kan ƙarin albashin nan cewa yake yana jiran gwamnatin tarayya ta fitar da tsarin da za a bi, amma yau wata nawa shiru kake ji.
"Mun gaji haka nan, kowa ya san halin da ake ciki, idan kana kashe N10 a wata yanzu ya koma N40 zuwa NN50, sannan kuɗin da muke samu ba su ƙaru ba, ina ake so mu sa kanmu?"

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sanya sabuwar ranar komawa makarantu, ta ba iyaye shawara

Gwamnatin Tinubu ya bada hutun Maulidi

A wani rahoton kuma gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar hutun Maulidin Annabi SAW na bana 2024.

Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 13 ga watan Satumba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262