Kano: Aminu Ado Ya Sake Daukar Kansa Sarki, Ya Gayyaci Musulmi Taron Maulidi a Fadarsa
- Duk da hukuncin kotu kan rigimar masarautu a jihar Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gayyaci al'ummar Musulmi
- Basaraken ya gayyaci Musulmi zuwa bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) a gobe Asabar 14 ga watan Satumban 2024
- Wannan na zuwa ne bayan tuge Aminu Ado Bayero daga sarauta da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a watannin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi gagarumar gayyata ta bikin Maulidi a fadarsa da ke Nassarawa.
Basaraken ya gayyaci al'ummar Musulmi domin bikin murnar ranar zagayowar haihuwar Manzon Allah (SAW).
Kano: Aminu Ado ya gayyaci Musulmi Maulidi
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ta wallafa a shafin Facebook.
Sanarwar ta ce za a gudanar da bikin Maulidin ne a gobe Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 da muke ciki.
Har ila yau, za a gudanar da bikin a fadar basaraken da ke Nassarawa da misalin karfe 8.00 na dare.
A ina za a gudanar da bikin Maulidin?
"Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, JP yana farin cikin gayyatar daukacin al'ummar Musulmi masoya shugaban mu Annabi Muhammad (S.A.W) zuwa wajen mauludin shugabanmu Annabi (S.A.W)."
"Taron Mauludin zai kasance a Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 a fadar Mai Martaba Sarkin Kano da ke Gidan Nassarawa da karfe 8:00 na dare."
"Allah ya ba da ikon halarta, Amin Summa Amin."
- Cewar sanarwar
Sarki Sanusi II ya roki al'ummar Kano alfarma
Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki ubangiji ya hada kan attajiran jihar guda biyu da ake ji da su domin kawo mata cigaba.
Sanusi II ya kuma roki al'umma su dage da addu'o'i domin Allah ya hada kan attajiran Kano, Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu.
Basaraken ya ce duk mai neman kawo rigima tsakanin attajiran na Kano ba son cigaban jihar ya ke yi ba ko kadan inda ya ce ba za su yi nasara ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng