Gwamnatin Bola Tinubu Ya Ba da Hutun Maulidin Annabi SAW na bana a Najeriya

Gwamnatin Bola Tinubu Ya Ba da Hutun Maulidin Annabi SAW na bana a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024 a matsayin ranar hutun Maulidin Annabi SAW na bana 2024
  • Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 13 ga watan Satumba
  • A madadin gwamnatin Bola Tinubu, ministan ya taya ɗaukacin al'ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana mai albarka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ba da hutun Maulidin Annabi Muhammad SAW na bana.

Gwamnatin ta sanar da ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024 daidai da 13 ga watan Rabi'ul Awwal, 1446H a matsayin ranar hutun Maulidi na bana.

Kara karanta wannan

Kano: Aminu Ado ya sake daukar kansa Sarki, ya gayyaci Musulmi taron Maulidi a fadarsa

Dr. Olubunmi Tunji-Ojo.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranar hutun Maulidi na bana a Najeriya Hoto: Dr. Olubunmi Tunji-Ojo
Asali: Twitter

Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Jumu'a, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta taya Musulmi murnar Maulidi

A madadin gwamnatin tarayya, ministan ya taya al'ummar musulmi na gida da na kasashen waje murnar zagayowar wannan rana.

A sanarwar mai ɗauke da sa hannun babban sakataren ma'aikatar cikin gida, Tunji-Ojo ya roki Musulmi da sauran ƴan Najeriya su yi koyi da kyawawan halaye.

Ya buƙaci ƴan Najeriya baki ɗaya su rungumi haƙuri, juriya da jajircewa musamman a wannan lokacin, sannan su sa Najeriya a addu'o'insu.

Tunji-Oji ya roki addu'a daga Musulmi

Da yake tura saƙon taya murna na musamman ga Musulmin Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci su yi amfani da wannan dama wajen yi wa ƙasar nan addu'a.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Dan majalisa ya ba gwamnatin Borno gudunmawar N100m

Ministan ya roƙi Musulmi su ci moriyar wannan lokaci mai albarka su roƙi Allah ya dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin Tinubu za ta karya farashi

Ku na da labarin gwamnatin tarayya ta ba 'yan kasuwa da masu ruwa da tsakiɓwa'adin kwanaki 30 su sauke farashin kayayyaki kafin ta fara daukar mataki.

Gwamnatin ta ce lallai za ta tilasta sauke farashin kayan masarufi a kasar da zarar wa'adin wata daya da ta ba 'yan kasuwar ya kare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262