Dan Sanda Ya yi Gumurzu da Yan Daba bayan Sun Taru za Su Kashe Shi

Dan Sanda Ya yi Gumurzu da Yan Daba bayan Sun Taru za Su Kashe Shi

  • Rundunar yan sanda a jihar Adamawa ta sanar da kama wasu matasa yan daba da ake zargi da kokarin kashe wani jami'in tsaro
  • Dan sandar ya shiga Kake NAPEP ne zuwa wani waje amma sai suka yi kokarin karkata zuwa wata hanya domin cutar da shi
  • An ruwaito cewa matukin Keke NAPEP da wasu matasa suka yi niyyar kashe dan sandan yayin da suka yi kokarin masa kwace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Yan sanda a jihar Adamawa sun kubutar da jami'insu da wasu yan daba suka yi kokarin hallakawa.

Rahotanni sun nuna cewa matasan da ake zargi sun dauki dan sandan ne a cikin Keke NAPEP da suke nuna cewa suna aiki ne da ita.

Kara karanta wannan

Mai garkuwa da mutane ya yanke sassan jikin budurwa bayan karbar kudin fansa

Yan sanda
An kama yan daba da suka nufi kashe dan sanda. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa dan sandar ya yi artabu da miyagun kafin ya samu taimakon wasu jami'ai.

Yadda 'yan daba suka so kashe dan sanda

Jaridar Leadership ta wallafa cewa dan sandan ya shiga Keke NAPEP ne daga Adamawa Unity Bridge zuwa Nasarawo a Jimeta.

Amma suna cikin tafiya sai matukin Keke NAPEP ya kauce hanya da gangan ya nufi hanyar Ribadu Square saboda mummunar manufa.

Bayan sun kauce hanya ne ake zargin matasan suka fara barazanar kashe 'dan sandan da kwace masa wayar hannu kuma daga nan aka fara rikici.

'Dan sanda ya yi gumurzu da yan daba

Matukin Keke NAPEP din yana dauke da wasu mutane biyu wadanda suke taimaka masa wajen yi wa fasinjan taron-dangi.

Sun hadu su uku suna son cin galaba a kan dan sandan ne sai ya yi ta maza, ya naushi matukin Keke NAPEP din, daga nan kuma suka fadi aka kama su.

Kara karanta wannan

Yadda matasa suka tsere daga kurkukun Bello Turji bayan ya saka ranar harbe su

Kakakin yan sanda a Adamawa, SP Sulaiman Yahaya Ngurore ya ce za a gurfanar da yan daban a gaban alkali domin a musu hukunci.

Sojoji sun kashe Halilu Sububu

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara kan yan bindiga masu garkuwa da mutane a yankin Arewacin Najeriya.

An samu labarin cewa rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar hallaka mai gidan Bello Turji, Kachalla Halilu Sububu a safiyar yau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng