Sheikh Jingir Ya Fadi Wadanda Suka 'Sanar da Shi' Tinubu bai San an Kara Kudin Fetur ba

Sheikh Jingir Ya Fadi Wadanda Suka 'Sanar da Shi' Tinubu bai San an Kara Kudin Fetur ba

  • Shugaban kungiyar Izala mai hedikwata a Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi karin haske kan maganar ƙarin kudin man fetur
  • Sheikh Jingir ya bayyana kafafen yada labaran da suka wallafa maganar inda ya ce su ya kamata a fara zagi kafin a iso kansa
  • Malamin ya bayyana dalilin da yasa mutane suka yi ca a kansa maimakon komawa ga kafafen da ya ce sun fara kawo labarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi karin haske kan maganar karin kudin fetur.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce mutane sun zage shi a kan cewa Bola Tinubu bai san an kara kudin man fetur ba duk da ba shi ya fara kawo labarin ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace Bello Yabo? Shehi ya yi maganar 'garkuwa' da shi da 'kamen' DSS

Sheikh Jingir
Sheikh Jingir ya yi karin haske kan maganar kudin fetur. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

Legit ta samo cikakken bayanin da malamin ya yi ne a cikin wani bidiyo da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a Facebook.

Bola Tinubu ya san da karin kudin fetur?

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi ikirarin cewa tun a karon farko kafafen yada labaran BBC, Daily Trust da NTA ne suka kawo labarin cewa Tinubu bai san an kara kudin fetur ba.

Malamin ya ce tun ranar Alhamis suka wallafa labarin shi kuma ya fada ranar Jumu'a da ya ga makiya tikitin Musulmi da Musulmi suna sukan gwamnatin Tinubu.

Sheikh Jingir ya ce ba a yi masa adalci ba

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce babu adalci a kan sukar da aka rika masa tun daga lokacin da ya fadi maganar.

Ya ce da akwai adalci kamata ya yi a fara da kafafen yada labaran da ya ce sun wallafa labarin kafin a iso kansa amma sai ka ware shi da zagi.

Kara karanta wannan

'Yan Kudu da Arewa sun hada kai, sun tunkari Tinubu kan tsadar man fetur

Kudin fetur: Jingir ya fadi dalilin zaginsa

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ya san mutane sun zage shi ne maimakon kafafen yada labaran saboda yana goyon bayan gwamnatin Musulmi da Musulmi.

Malamin ya kuma tabbatar da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi.

Jingir ya bukaci maido tallafin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izalar Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya roki Tinubu kan cire tallafin mai.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya roki Shugaba Tinubu ya dawo da tallafin mai don samun sauki ga al’ummar Najeriya da ke wani hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng