"Baki Ke Yanka Wuya": Bello Turji Ya Taɓo Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Pantami

"Baki Ke Yanka Wuya": Bello Turji Ya Taɓo Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Pantami

  • Bello Turji ya taɓo tsohon ministan sadarwa, Sheikh Farfesa Isa Pantami a bidiyon karshe da ya fitar kan batun haraji
  • Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi ikirarin yana da wa'azin da Pantami ya ce duk wanda ya shiga gwamnati to ya bar Musulunci
  • Turji ya kuma roki babbban hafsan sojin Najeriya ya taimaka ya ba Murtala Asada muƙami ko da na shugaban ƴan banga ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - A sabon bidiyon da ya saki kwanan nan, Bello Turji ya taɓo tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.

Gawurtaccen ɗan bindigar ya bayyana cewa Pantami ya ba da fatawa a karatunsa na baya cewa duk wanda ya shiga gwamnati to ya bar da'irar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Kasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya turo saƙo kan harajin N50m da ya sa a Zamfara

Farfesa Isa Pantami.
Bello Turji ya sako batun Sheikh Pantami a sabon bidiyon da ya saki Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Asali: Twitter

A faifan bidiyon wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta musamman Facebook, Bello Turji ya ce wannan fatawa ta hau kan Pantami tun da ya karɓi kujerar minista.

Turji ya aika sako ga hafsan sojin Najeriya

Ɗan ta'adda ya kuma buƙaci babban hafsan sojojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya ba babban malamin nan, Murtala Asada wani muƙami a cikin jami'an tsaro.

"Shugabanmu mai albarka Chirstopher Musa ina kira gare ka da babbar murya, dan Allah ka taimaka mana Murtala Asada, ko da ba ka iya ba shi wani muƙami, ka ba shi na shugaban ƴan banga."
"Dan Allah dan Annabi (ka ba shi muƙami) ya shigo, ka ba shi wani muƙami ya shigo sai ya gani, yanzu na ga muƙami yake so to ka ba shi ya taho," in ji Bello Turji.

Kara karanta wannan

NAF: Jirgin sojoji ya yi luguden wuta kan ƴan bindiga, ya hallaka da dama a Arewa

Kalaman Bello Turji kan Sheikh Isa Pantami

Da yake magana kan Pantami, Turji ya ce yana da karatuttukan tsohon ministan a lokacin da yake cewa duk wanda ke cikin gwamnati ɗagutu ne kafiri ne.

"Ka duba ministan sadarwa (wanda ya sauka), ina da wa'azin shi da yake cewa duk wanda ke cikin gwamnati ƙafiri ne, ɗagutu ne.
"Amma yanzu tun da an ba shi ministan sadarwar yaushe rabon da ka ji shi? Kenan shi ma yanzu ya kafurta ya tabbatar ya yi ridda kenan, saboda haka muke gode wa Allah," in ji Turji.

Turji ya tabbatar da batun haraji a Zamfara

A wani rahoton hatsabibin ɗan bindigar nan, Bello Turji ya tabbatar da sa harajin N50m a garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Shinkafi a Zamfara

A wani faifan bidiyo da ke yawo a midiya, Turji ya ce ya sa wannan harajin ne saboda kashe ƴan uwansa da wasu shanu da sojoji suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262