"Ba Fashe wa Dam Ta Yi ba:" Gwamnati Ta Fadi Ainihin Dalilin Ambaliya a Maiduguri

"Ba Fashe wa Dam Ta Yi ba:" Gwamnati Ta Fadi Ainihin Dalilin Ambaliya a Maiduguri

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa aka samu mummunar ambaliyar ruwa a jihar Borno a farkon makon nan
  • Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Joseph Utsev ne ya yi karin bayanin, yayin da gargadi wasu jihohi
  • Farfesa Utsev ya bayyana cewa ba ballewa madatsar ruwa ta Alau ta yi ba, amma an samu ruwa mai yawan gaske a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ruwan da ke shiga madatsar Alau ne ya fi karfinta a bana, wanda ya sa ya nemi hanyar fita zuwa cikin gari.

Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na kasa, Farfsa Joseph Utsev ne ya yi karin bayanin a ganawarsa da manema labarai kan ambaliyar Maiduguri.

Kara karanta wannan

Bayan ambaliya ta kashe mutum 37, gwamnati ta ba da umarni kan madatsar Alau

Borno
An gano dalilin ambaliya a Maiduguri Hoto: Umar AbuSufyan Yusuf/Mustapha Alhaji Tijjani
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro Ministan ya kara da cewa ruwan da aka samu a bana ya yi yawan gaske wanda ya jawo aka samu karuwar ruwa daga kogin Ngadda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya: Wane hali madatsar Alau ke ciki?

Joseph Utsev ya bayyana cewa madatsar ruwa ta Alau da ta haddasa ambaliya a jihar Borno na nan garau babu abin da ya same ta.

Jaridar The Nation ta tattaro Ministan ya ce ruwan da ya fito daga madatsar hauro wa ya yi, amma bai lalata madatsar Alau ba kamar yadda wasu ke yada wa.

Gwamnati ta gargadi jihohin Kudu kan ambaliya

Gwamnatin Bola Tinubu ta gargadi jihohin Kudancin kasar nan da su kwana cikin shirin afkuwar gagarumar ambaliya.

Farfsa Utsev ya yi gargadin a Jere, jihar Borno, inda ya ce ruwan da ya yi ta'adi a Maiduguri na kan hanyarsa ta fantsama wasu jihohin

Kara karanta wannan

Magidanci na neman matarsa da ƴaƴansa 5, ana fargabar sun bace a ambaliyar Maiduguri

Za a inganta madatsar Alau bayan ambaliya

A baya kun samu labarin cewa gwamnatin tarayya ta ce tuni ta bayar da umarnin inganta madatsar ruwa ta Alau domin ba ta damar daukar karin ruwa mai yawa a gaba.

Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ce za ta dauka domin dakile afkuwar mummunar ambaliya da aka fuskanta a Maiduguri a ranar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.