Kasurgumin Ɗan Bindiga Bello Turji Ya Turo Saƙo kan Harajin N50m da Ya Sa a Zamfara

Kasurgumin Ɗan Bindiga Bello Turji Ya Turo Saƙo kan Harajin N50m da Ya Sa a Zamfara

  • Hatsabibin ɗan bindigar nan, Bello Turji ya tabbatar da sa harajin N50m a garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Shinkafi a Zamfara
  • A wani faifan bidiyo da ke yawo a midiya, Turji ya ce ya sa wannan harajin ne saboda kashe ƴan uwansa da wasu shanu
  • Tun farko dai Bula Bukarti ne ya fara fasa maganar, inda ya ce ɗan bindigar ya sa harajin a matsayin diyyar shanunsa da sojoji suka harbe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gawurtaccen ɗan bindigar nan, Bello Turji ya tabbatar da sa harajin N50m kan mutanen garin Moriki a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Ƙasurgumin ɗan bindigan ya kuma caccakin lauyan nan ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin dan adam, Bulama Bukarti kan tsoma bakin da ya yi a batun harajin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'an sojoji a wani farmaki a jihar Arewa

Sojojin Najeriya.
Gawurtaccen ɗan bindiga, Bello Turji ya tabbatar da sanya harajin N50m a Zamfara Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna huɗu zuwa biyar da Bello Turji ya fitar kuma aka wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon an ga Turji ɗauke da babbar bindiga kewaye da yaransa ƴan bindiga waɗanda suke sanye da kakin sojoji da manyan bindigu a hannunsu.

Bulama ya fasa batun harajin N50m

Tun farko dai Bulama ya bayyana a shafinsa na X cewa Bello Turji ya ƙaƙaba harajin N50m kan al'ummar garin Moriki a jihar Zamfara.

Lauyan ya ƙara da cewa mutanen garin sun ƙoƙarin rarrashin kasurgumin ɗan bindigar kuma ya amince ya rage harajin daga N50m zuwa N30m.

A cewar Bulama, Turji ya buƙaci su biya kuɗin a matsayin diyyar shanunsa da sojoji suka kashe kuma ya ba su wa'adin 11 ga watan Satumba su kawo kuɗin.

Bello Turji ya tabbatar da lamarin Moriki

Kara karanta wannan

NAF: Jirgin sojoji ya yi luguden wuta kan ƴan bindiga, ya hallaka da dama a Arewa

Da yake martani ga Bulama Bukarti, hatsabibin ɗan bindigar ya ce:

"Eh kwarai da gaske, bai yi ƙarya ba kuma bai yi kuskure ba, Bello Turji ya yi magana da ƴan Moriki amma na ji ya ce wai saboda an korar mana shanu, to ba haka aka yi ba.
"Eh tabbas na azawa ƴan Moriki harajin N50m. Ku ji mutanen Moriki a nan aka haife ni kuma a nan aka haife ku, ba a taɓa kawo wani soja daga Enugu ko Fatakwal ya kashe mana ƴan uwa domin ku ji daɗi, mu kuma mu zuba muku ido."

Turji ya kuma yi iƙirarin cewa an harbe wasu daga cikin mutanensa a gaban Masallacin Jumu'a a Birnin Yero.

Mahara sun shiga asibiti a Katsina

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun kai hari babban asibitin da ke ƙaramar hukumar Kurfi a jihar Katsina ranar Laraba da ta gabata da daddare.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa cikin daji, sun hallaka ƴan bindigar da suka addabi mutane a Arewa

Bayanai sun nuna maharan sun harbi mai gadi, sun sace mata hudu a ciki har da matar wani likita da ke aikin dare a asibitin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262