Ambaliyar Maiduguri: Mutanen da Aka Ceto daga Gidaje Sun Haura 3,600
- Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno ta bayyana cewa har yanzu ana aikon ceto jama'a a Maiduguri
- Zuwa yammacin Alhamis, an samu nasarar ceto akalla mutane 3,682 da mamakon ruwan ya tare a cikin gidajensu
- Shugaban hukumar SEMA, Barkindo Mohammed ya bayyana cewa har yanzu jami'ansu na aikin ceto jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayyana ceto mutane 3,682 da ambaliyar ruwa ta tare a jihar Borno.
Shugaban hukumar agajin Borno, Barkindo Mohammed ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Juma'a, inda ya ke bayani kan halin da ake ciki a Maiduguri.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa har yanzu jami'an hukumar bayar da agajin da sauran masu taimako na kokarin ceto mutanen da ambaliyar ta rutsa a Maiduguri.
Ambaliya: Yadda ake ceto mutanen Maiduguri
Pulse Nigeria ta wallafa cewa shugaban SEMA na Borno, Barkindo Mohammed ya ce ana amfani da jiragen ruwa da motocin hukumar kashe gobara wajen aikin ceto mutane.
Jami'an sojoji da yan sanda da masu aikin sa kai ne ke aikin taimakon ceto wadanda ba a san halin da su ke ciki ba kwanaki bayan ambaliyar.
Matakan taimakon jama'ar da ambaliya ya rutsa
Zuwa yanzu adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri ya haura miliyan biyu, kamar yadda hukumar SEMA a jihar ta fada.
Shugaban hukumar, Barkindo Mohammed ya ce an bude sansanoni 14 a hukumance da wasu kwarya-kwaryar wuraren ajiye jama'a domin taimakonsu.
Ambaliya: Dan majalisa ya mika taimakon N100m
A wani labarin, kun ji yadda dan majalisar wakilai mai wakiltar Biu/Bayo/Shani/Kwaya/Kusar, Mukhtar Betara ya mika tallafin N100m ga al'ummar Maiduguri.
Dan majalisar ya bayar da gudunmawar lokacin da ya ziyarci Maiduguri domin gani irin ta'asar da ambaliyar ruwa ta yi wa al'ummar yankin sama da miliyan biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng