Wani Jirgi Ya Gamu da Haɗari a Najeriya, An Nemi Wasu Fasinjoji An Rasa

Wani Jirgi Ya Gamu da Haɗari a Najeriya, An Nemi Wasu Fasinjoji An Rasa

  • Wasu mutum biyu da ke kasuwancin itace sun nutse a ruwa a wani haɗarin kwale-kwale da ya rutsa da su a jihar Ogun
  • Mai magana da yawun ƴan sandan Ogun ta ce har yanzun ba a gano gawarwakin mutane biyu ba, sauran kuma sun tsira
  • Rahotanni sun nuna cewa haɗarin ya afku ne a lokacin da igiyar ruwa ta rinjayi kwale-kwalen sai ya kife a tsakiyar teku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Wasu mutane biyu sun mutu sakamakon haɗarin jirgin ruwa a yankin karamar hukumar Ipoki ta jihar Ogun.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Ogun, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: NEMA ta bayyana adadin mutanen da suka rasu a jihar Borno

Taswirar jihar Ogun.
Mutum 2 sun nutse a wani haɗarin jirgin ruwa da ya afku a jihar Ogun Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ta ce rundunar ƴan sandaI ta samu rahoton faruwar haɗarin ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba, 2024, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kakakin ƴan sanda ta ce wasu mutum biyu daga ƙauyen Ilepa ne suka kai rahoton haɗarin ga DPO na ƴan sandan yankin.

Yadda jirgin ya kife a kogi

A rahoton Daily Post, Odutola ta ce:

"Wasu mutane biyu, Awhanse Jimoh da Ahohe Jimoh, daga kauyen Ilepa da ke Ipokia, sun kai rahoto ga DPO na ƴan sanda cewa wasu masu sayar da itace sun nutse a kogi.
"Sun ce ƴan kasuwar biyu sun ɗauko itacen girki a rafin Gbodo Jego da nufin zuwa jamhuriyar Benin domin sayarwa, kwatsam haɗarin ya rutsa da su.
"Suna cikin tafiya domin haye kogin, ba za to wani ruwa mai ƙarfi ya kifar da jirgin ruwan da suke ciki, an yi koƙarin ceto su amma mutum biyu kaɗai aka gano."

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Ƴan sanda sun fara bincike kan haɗarin

Omolola Odutola ta ƙara da cewa duk da ƙoƙarin ceto waɗannan masu itacen, har yanzu ba a iya gano gawarwakinsu ba amma ana ci gaba da bincike.

Ya kuma tabbatar da cewa ƴan sanda sun fara bincike domin gano musabbabin haɗarin da kuma ɗaukar bayanan mutum biyun da suka tsira da ransu.

Haɗarin jirgin ruwa ya laƙume rayuka 4

A wani rahoton kuma hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutum hudu, wasu mutum biyu sun ɓace a yankin ƙaramar hukumar Lafia a jihar Nasarawa.

Rahoto ya nuna kwale-kwalen ya ɗauko ƴan kasuwa akalla 25 da kayayyaki a lokacin da ya nutse a kusa da ƙauyen Ashangwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262