'Yan Bindiga Sun Kai Hari Babban Asibiti, Sun Yi Awon Gaba da Mata a Arewa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Babban Asibiti, Sun Yi Awon Gaba da Mata a Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai hari babban asibitin da ke ƙaramar hukumar Kurfi a jihar Katsina ranar Laraba da ta gabata da daddare
  • Bayanai sun nuna maharan sun harbi mai gadi, sun sace mata hudu a ciki har da matar wani likita da ke aikin dare a asibitin
  • Ana ganin dai harin wani babban koma baya ne a Kurfi saboda yadda mutanen garin ke ƙoƙarin kare kansu daga ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki babban asibitin Kurfi da ke ƙaramar hukumar Kurfi a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun harbi mai gadi, sannan suka sace mata huɗu ciki hada matar wani likita wanda ke zaune a cikin asibitin.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya 'kashe' budurwar da zai aura Naja'atu Ahmad a jihar Kano

Malam Dikko Radda.
Yan bindiga sun sace mutum 4 a harin da suka kai asibitin Kurfi a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda PhD
Asali: Facebook

Wasu majiyoyi sun ce ƴan bindigar sun fara zuwa asibitin ba tare da makamai ba da misalin ƙarfe 10:45 na daren ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani ƴan uwansu suka ƙaraso ɗauke da makamai yayin da mai gadin ya yi ƙarfin hali, ya kulle ƙofar shiga.

Yadda ƴan bindigar suka kutsa asibitin

Ƴan bindigar sun haura ta katanga, suka harbi mai gadin a ciki, da farko an yi tunanin ya mutu amma daga baya aka ba shi agaji, sannan aka garzaya da shi wani asibiti a Katsina.

An ce maharan sun yi yunƙurin ɗaukar Mustapha Hamza, wani ma'aikacin wucin gadi da ke aikin dare a lokacin amma Allah ya taimake sa ya tsira, suka tafi da matarsa.

Bayanai sun nuna Hamza ya shiga asibitin da dare ne bayan an kira shi ya yi tiyata, sannan matarsa ta raka shi saboda tana jin tsoron zama a gida ita kaɗai.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun ceto mutum 20 da aka sace

Harin dai ba ƙaramin koma baya ba ne a garin Kurfi, wanda ya yi ƙauren suna wajen kare kansa daga ƴan bindiga.

Wane mataki mahukunta suka ɗauka?

Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaro, shugaban ƙaramar hukumar Kurfi, Mannir Shehu Wurma, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace domin kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.

Wani mazaunin Kurfi da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan harin akwai sakacin jami'an tsaro.

A cewarsa, tun farko an ga alamun ƴan bindiga na shirin kawo harin kuma an sanar da jami'an tsaro amma ba su ɗauki wani mataki ba.

"Ba na son magana sosai saboda abubuwan da suka shafi tsaro ba a son bayyana su, amma a taƙaice ina ganin wannan harin da aka kawo mana akwai sakacin jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun samu nasara kan 'yan bindiga a jihar Neja

"Sun ɗauki mutum huɗu duk mata, alamu sun nuna likita suka so sace wa amma ya gudu. Muna kira ga gwamnati ta ƙara dagewa wajen tsaron al'umma," in ji shi.

Ƴan bindiga sun kutsa asibiti a Kaduna

A wani labarin kun ji cewa ƴan bindiga sun shiga wani asibitin dakin shan magani a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Shugaban rundunar ƴan banga na yankin ya ce maharan sun fara shiga wata maƙarantar sakandire kafin daga bisani su shiga asibitin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262