Sabon Albashi: Gwamnan Kano Ya Fadi Lokacin da Zai Fara Biyan Ma'aikata N70000

Sabon Albashi: Gwamnan Kano Ya Fadi Lokacin da Zai Fara Biyan Ma'aikata N70000

  • Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta bai wa ma’aikatan jihar tabbacin biyan sabon mafi karancin albashi
  • Abba Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara biyan ma'aikata mafi karancin albashi na N70,000 daga mako mai zuwa
  • Shugaban ma’aikatan gwamnatin Kano, Abdullahi Musa ya tabbatar da hakan tare da yin karin bayani kan yadda aiwatar za ta kasance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana cewa jiharsa ce za ta fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 11 ga Satumba a wajen wani taron karawa juna sani da aka shirywa kungiyar NLC da sauran kungiyoyinta na reshen Kano.

Kara karanta wannan

N70,000: Gwamna ya yi alkawarin karin albashi, ya kafa sharadi

Gwamnan Kano yayi magana a kan aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.
Gwamna Abba Yusuf ya yi magana kan lokacin fara biyan ma'aikatan Kano sabon mafi karancin albashi. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Facebook

Gwamna Abba zai fara biyan N70,000

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gwamnatin Kano, Abdullahi Musa, ya tabbatar da cewa jiharsa ce za ta fara aiwatar da sabon albashin, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Domin nuna irin muhimmancin da gwamnati ke da shi wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashi, za mu kasance a Kaduna domin taron karawa juna sani.
Za mua halarci wannan taron ne musamman domin magance matsalar da ta shafi mafi karancin albashi a jihar Kano.”

- A cewar gwamnan.

Taron kwamitin albashin Kano a Kaduna

Gwamna Yusuf ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi a jihar Kano a watan Agusta 2024.

A wajen taron, Abdullahi Musa ya bayyana cewa:

“Dukkanin 'yan kwamitin ba da shawara na nan Kaduna domin tattaunawa kan batun mafi karancin albashin da kuma cimma matsaya tare da fara biya nan da mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

Wani Malamin Addini ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira, gwamna ya ɗauki mataki

"Za mu isar da rahotanmu ga gwamna domin ya yi aiki da shi. Da izinin ubangiji mu ne za mu fara biyan sabon mafi karancin albashi."

Abba ya gabatar da karin kasafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf ya gabatar da karin kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar dokokin Kano da ya kunshi sabon mafi karancin albashi.

Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Isma'il Falgore ya karanta wasikar da Abba Kabir Yusuf ya tura musu karin karin kasafin da kuma batun fara biyan ma'aikata albashin N70,0000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.