'Ya Nuna Jarumtaka': Atiku Ya Kadu da Mutuwar Babban Sarki a Kudancin Najeriya

'Ya Nuna Jarumtaka': Atiku Ya Kadu da Mutuwar Babban Sarki a Kudancin Najeriya

  • Atiku Abubukar ya aika sakon ta'aziyya ga al'ummar kasar Ijesha da ke jihar Osun bisa rasuwar babban sarkinsu, Owa Obokun
  • A yau Alhamis, 12 ga watan Satumbar 2024 ne aka sanar da rasuwar Owa Obokun na Ijeshaland, Oba Gabriel Aromolaran
  • Tsohon shugaban kasar wanda ya ce ya ya bayyana marigayi Aromolaran a matsayin jajurtaccen basarake kuma suruki na gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana matukar alhininsa game da rasuwar Owa Obokun na Ijeshaland, Oba Gabriel Aromolaran.

A wata sanarwa da Atiku ya fitar, ya tuno da irin soyayyar da marigayi Aromolaran ya nuna masa, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtacce mai kishin al'ummar Ijesha.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki bayan fara raɗe raɗin ya rasu

Atiku ya yi alhinin rasuwar sarkin kasar Ijesha
Atiku Abubakar ya aika sakon ta'aziyya ga al'ummar Ijesha kan rasuwar Sarki Aromolaran
Asali: Twitter

Atiku ya yi alhinin rasuwar sarki

Atiku, wanda ya fitar da sanarwar a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya wallafa ta'aziyyarsa hade da hoton da ya dauka tare da basaraken da gwamnan Osun, Ademola Adeleke.

An rahoto cewa matar Atiku, Titi 'yar garin Ilesa ce da ke Osun, dalilin da ya sa tsohon mataimakin shugaban ya kira basaraken da 'suruki.'

Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya wallafa cewa:

“A cikin alhini na samu labarin rasuwar Owa Obokun na kasar Ijesha, Oba Gabriel Adekunle Aromolaran."

Basarake ya samu yabo daga Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kalaman yabo ga marigayi Oba Aromolaran yana mai cewa:

“Marigayi Owa ya fi karfin suruki a waje na. Duk lokacin da na ziyarce shi, yana yi mani maraba a matsayin dansa. Dukanmu mun ƙaunace shi sosai.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa Akpabio ya kadu da ambaliya a jihohin Arewa, ya sha alwashi

“Ya kasance babban sarki kuma ya nuna jarumtaka, yakana, da kuma tabbatar da dorewar kyakkyawar al'adar 'yan Ijesha."

A madadin matarsa, Titi, Atiku ya mika sakon ta'aziyya ga majalisar Owa da kuma daukacin al'ummar Ijesha musamman jinin masarautar.

Sarkin kasar Ijesha ya rasu

Tun da fari, mun ruwaito cewa wani sarki mai daraja ta daya a jihar Osun, Owa-Obokun na kasar Ijesa, Oba Gabriel Adekunle Aromolaran, ya rasu.

An bayyana rasuwarsa ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Asiwaju na kasar Ijesa, Cif Yinka Fasuyi, a ranar Alhamis a Osogbo, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.