'Yan Bindiga Sun Tare Babbar Hanya a Arewa, Sun Sace Matafiya Masu Yawa
- Wasu ƴan bindiga sun tare babban titin hanyar Gusau zuwa Funtua da sanyin safiyar ranar Alhamis, 12 ga watan Satumban 2024
- Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun zo ne a kan babura masu yawa inda suka riƙa tafiya da mutane cikin daji
- Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ba ta bayyana adadin mutane nawa ƴan bindigan suka ɗauke ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun sace matafiya masu yawa a kan titin garin Gusau zuwa Funtua.
Miyagun ƴan bindigan sun sace mutanen ne bayan sun tare hanyar a ranar Alhamis da safe.
Yadda ƴan bindiga suka tare hanyar
Tashar Channels tv ta ce wani matafiyi a hanyar mai suna Yusuf Tsafe ya gaya mata cewa ƴan bindigan sun tare titin ne da safiyar ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun tare hanyar ne a wajen yankin Tazame.
A cewarsa ƴan bindigan waɗanda suka zo a kan babura kusan 50 kowane ɗauke da mutum uku sun sace matafiya masu yawan gaske.
"Sun zo kan hanyar ne wajen ƙarfe 7:00 na safe kuma har zuwa wajen ƙarfe 9:00 suna nan. Mun ajiye motocinmu a bakin titi muna jiran sojoji su kore su. Mun ga ƴan bindiga suna tafiya da mutane zuwa cikin daji."
"Motar sojoji ta wuce zuwa wajen, mun jiyo ƙarar harbe-harben bindiga amma har yanzu ba a buɗe hanyar ba. Har ya zuwa yanzu babu motar da aka bari ta wuce."
- Yusuf Tsafe
Wani matafiyi ya ƙara tabbatar da cewa ƴan bindiga sun tare hanyar Magazu zuwa Kucheri da ta haɗe da hanyar Gusau zuwa Funtua da safiyar yau.
"Sojoji sun ce mana mu tsaya saboda ƴan bindiga sun tare hanyar, har yanzu muna jira su gyara hanyar."
- Wata majiya
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa suna haɗa rahoto ne kan abin da ya faru.
"Eh lamarin ya faru da safe, yanzu haka muna kan haɗa rahoto ne kan abin da ya faru. Mu na ci gaba da tattara bayanai. Ba za mu iya cewa an ɗauki mutane ko ba a ɗauka ba har sai mun kammala tattara bayanai."
- ASP Yazid Abubakar
Mutanen gari sun hallaka ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutanen gari sun hallaka aƙalla ƴan bindiga 37 a ƙauyen Matusgi a ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.
Mutanen sun samu nasarar ne bayan sun yi fito na fito da ƴan bindigan waɗanda suka farmaki ƙauyen da niyyar sace mutane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng