NNPP Ta Fito da Mace a Matsayin 'Yar Takarar Shugabar Karamar Hukumar Kano

NNPP Ta Fito da Mace a Matsayin 'Yar Takarar Shugabar Karamar Hukumar Kano

  • Jam'iyya mai mulki a Kano ta fitar da yan takara akalla 484 a zaben kananan hukumomi da za a gudanar nan gaba kadan a jihar
  • Daga cikin masu neman mukamai daban-daban, NNPP ta tsayar da mace guda daya, Sa'adatu Salisu a takarar shugabar karamar hukuma
  • A ranar 26 Oktoba ne hukumar zaben mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) za ta gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP ta kammala fitar da yan takarar da za su tsaya takara a zaben kananan hukumomin da ke tafe a jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Yan takarar NNPP 20 na ta'ammali da kwayoyi a kano? NDLEA ta yi karin haske

An tsayar da mutane 484 a mukamai daban-daban da su ka hada da kansiloli da shugabannin kananan hukumomi 44 a jihar.

Jihar
NNPP ta fitar da mace 1 a takarar zaben kananan hukumomi Hoto: Salisu Yahaya Hotoro
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa daga cikin wadannan 'yan takara, akwai mace guda daya mai suna, Sa’adatu Salisu daga Tudunwada a Kano ta Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta kammala tantance yan takara

Shugaban jam'iyyar NNPP a Kano, Dr. Hashim Sulaiman Dungurawa ya bayyana cewa an tantance yan takararta bisa tsari da doka.

Dr. Dungurawa ya kara da cewa tsarin da suka bi wajen fitar da yan takarar sun hada da 'yar nune wanda aka amince da shi a tsarin dimukuradiyya.

Jam'iyyar NNPP na son shigar mata siyasa

Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa ta na goyon bayan mata shiga siyasa, saboda haka ne ma su ka tsayar da Hajiya Sa’adatu Salisu.

Kara karanta wannan

"Zai yi wahala," NNPP ta yi martani kan samun 'yan kwaya a cikin 'yan takararta

Ya ce an fitar da Hajiya Sa'adatu ne saboda jajircewarta da iya gudanar da aiki, inda ya bayyana yakinin za ta iya kawo ci gaba.

NNPP ta magantu kan 'yan takararta

A baya kun ji cewa jam'iyyar NNPP a Kano ta musanta cewa an samu wasu daga cikin 'yan takararta da ta'ammali da miyagun kwayoyi yayin da ake tantance su a Kano.

Shugaban jam'iyyar a Kano, Dr. Hashim Dungurawa ne ya bayyana haka, inda ya ce ba sa tafiya da masu shaye-shaye, domin tafiyar Kwankwasiyya ta samar da ilimi da ci gaba ce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.