Gwamnatin Kano Ta Sanya Sabuwar Ranar Komawa Makarantu, Ta Ba Iyaye Shawara

Gwamnatin Kano Ta Sanya Sabuwar Ranar Komawa Makarantu, Ta Ba Iyaye Shawara

  • Gwamnatin jihar Kano ta sanya sabuwar ranar da ɗaliban makarantun firamare da na gaba da firamare za su koma karatu
  • A wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilmi ya fitar, ya ce za a koma ne ranakun 15 da 16 ga watan Satumba
  • Ma'aikatar ta kuma shawarci ɗalibai da su guji zuwa makarantu da haramtattun abubuwa sannan su kasance masu bin doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta sanya sabuwar ranar da ɗalibai za su koma makarantun firamare da na gaba da firamare a faɗin jihar.

Gwamnatin ta sanya ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba a matsayin sabuwar ranar da ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu a za su koma a faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Wani Malamin Addini ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira, gwamna ya ɗauki mataki

Gwamnatin Kano ta sanya ranar komawa makarantu
Gwamnatin Kano ta sanya lokacin da dalibai za su koma makarantu Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ɗalibai za su koma makaranta a Kano

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilmi ta jihar, Balarabe Kiru ya fitar wacce hadimin Gwamna Abba Kabir ya sanya a shafinsa na X ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa ɗaliban da ke makarantun je ka ka dawo za su koma makaranta a ranar Litinin, 16 ga watan Satumban 2024.

Hakan na zuwa ne bayan a ranar Asabar, 7 ga watan Satumban 2024z, kwamishinan ilmi, Alhaji Umar Doguwa ya sanar da ɗage ranakun komawa makarantu a faɗin jihar.

Ma'aikatar ilmin Kano ta ba iyaye shawara

A cikin sanarwar, ma'aikatar ilmi ta jihar ta buƙaci iyayen ɗalibai da su kula da sabuwar ranar komawa makarantun domin tabbatar da sun yi amfani da ita.

Kara karanta wannan

Ana jimamin ambaliyar Maiduguri, ruwa ya katse garuruwa 5 a jihar Kaduna

Ta kuma shawarci ɗalibai da su guji zuwa makarantu da haramtattun abubuwa irin su wuƙa ko reza sannan su yi biyayya ga dokokin makaranta.

Gwamnatin Kano ta bankaɗo ɓarayi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ce ta bankaɗo yadda wasu ma'aikatan lafiya ke sacewa tare da sayar da magunguna da wasu kayayyakin kiwon lafiya a jihar.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakan daƙile karkatar da magunguna da kayayyakin kiwon lafiya daga asibitoci da cibiyoyin lafiya mallakar gwamnatin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng