NAF: Jirgin Sojoji Ya Yi Luguden Wuta kan Ƴan Bindiga, Ya Hallaka da Dama a Arewa
- Jirgin rundunar sojojin saman Najeriya ya saki ruwan bama-bamai kan ƴan bindiga a kauyen Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja
- A wata sanarwa da NAF ta fitar ranar Alhamis, ta ce jirgin ya yi nasarar kashe akalla ƴan bindiga 28 a harin
- Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya kai ɗauki ne domin taimakawa sojojin ƙasa waɗanda suka fara musayar wuta da ƴan bindigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Jirgin yaƙin rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ya sheƙe ƴan bindiga akalla 28 a garin Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.
Jirgin yaƙin ya yi ruwan wuta tare da kashe ƴan bindigar waɗanda ke musayar wuta da jami'an tsaro ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, 2024.
Mataimakin daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na NAF, Kyaftim Kabiru Ali ne ya bayyana hakan a wata sanarwa yau Alhamis, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin yaƙi ya kaiwa sojoji ɗauki
Kyaftin Kabiru ya ce jirgin ya yi wa maharan luguden wuta bayan sojojin ƙasa da ke fafatawa da ƴan bindigar sun nemi a kawo masu ɗauki.
"Lokacin da jirgin yaƙin ya isa wurin ya hangi ƴan ta'adda na musayar wuta da abokan aiki sojojin ƙasa. Bayan tantance ɓangaren da sojoji suke tsaye, nan take jirgin ya saki wuta kan ƴan bindigar.
"Ruwan bama-baman jirgin ya yi abin da ake so, ya hallaka gomman ƴan bindiga wanda zuwa yanzu an gano gawar ƴan ta'addda 28 a wurin, sannan an lalata kayan aikinsu."
A cewar Kyaftin Kabir Ali, nasarar da rundunar NAF ta samu ta ƙara fito da kudirinta na kare ƙasa da taimakawa ayyukan ‘yan uwa sojoji da sauran hukumomin tsaro.
Sojoji za su dawo da zaman lafiya
Ya ce sojojin sama ba za su yi ƙasa a guiwa ba a ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga, ta'addanci, tada ƙayar baya da sauran miyagun laifuka, rahoton Punch.
Bugu ɗa ƙari, ya tabbatar da cewa sojojin sama za su ci gaba da kai samame tare da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro domin murƙushe duk wata barazanar tsaro.
Sojoji sun kai farmaki sansanin ƴan bindiga
A wani rahoton kuma sojoji sun hallaka ƴan bindiga huɗu, sannan sun kuɓutar da mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna
Rahotanni daga mazuana yankin Kasangwai sun nuna cewa sojojin sun farwa ƴan bindigar ne a maboyarsu ta jeji ranar Litinin da ta gabata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng