Ambaliyar Maiduguri: NEMA Ta Bayyana Adadin Mutanen da Suka Rasu a Jihar Borno
- An fara tattara bayanai da alƙaluman waɗanda suka mutu a mummunar ambaliyar da ta faru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno
- Mai magana da yawun hukumar ba da agaji ta ƙasa (NEMA), Ezekiel Manzo, ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 30 zuwa yanzu
- Mazauna Maiduguri sun ce da yiwuwar adadin ya haura haka domin har yanzun akwai waɗanda ba a gani ba ciki har da ƙananan yara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 30.
Daruruwan gidaje ne lamarin ya rutsa da su, wanda kuma ya jawo hasarar dukiya da suka hada da filayen noma, wuraren zama da wuraren kasuwanci.
Mutum nawa suka rasu a ambaliyar Maiduguri?
Daily Trust ta ce ibtila'in ya afku ne sakamakon kwararar ruwa daga Alau Dam, wanda ya cika ya batse sannan ya fara sakin ruwa daga nisan kilomita 10 zuwa Maiduguri.
Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Ezekiel Manzo, ya shaida wa AFP cewa, “Mutane 30 ne suka mutu."
Mazauna garin sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa saboda har yanzun akwai waɗanda ba a gano ba ciki har da ƙananan yara.
Mutanen Maiduguri sun ce adadin ya haura haka
Tasiu Abdullahi, mazaunin daya daga cikin yankunan da lamarin ya shafa a Gwange ya ce:
"Babu wanda ke da ainihin adadin mutanen da suka mutu sakamakon wannan jarabawa ta ambaliya,"
Wani direban motar haya, Babagana Modu, ya bayyana cewa waɗanda suka mutu za su iya kai wa 60 ko sama da haka.
Wuraren da ambaliya ta yi ɓarna
Muhimman wuraren da abin ya shafa sun hada da kasuwar Litinin, fadar Shehun Borno, Shehuri, Gwange, Adamkolo, Gamboru, Fori, Bulabulin, gidan waya, Moromoro, da gadar Kwastam.
Ruwan ya shafe makabartar Gwange, inda aka ga gawarwaki suna yawo a kan tituna a cewar rahoton jaridar Punch.
Haka zalika marasa lafiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) sun makale yayin da wasu sassan ginin suka cika maƙil da ruwa.
NiMET ta ankarar da wasu jihohi
A wani rahoton na daban yayin da al'ummar Borno ke fama da matsalar ambaliya da ta nemi shafe Maiduguri, hukumar kula da yanayi (NiMET) ta yi sabon hasashe
A sabon hasashen, NIMET ta bayyana cewa za a samu mamakon ruwa kamar da bakin kwarya hadi da tsawa na kwanaki uku a jere a wasu jihohin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng