EFCC Ta Gano Musabbabin Ta'addanci, An Shirya Daukar Matakai

EFCC Ta Gano Musabbabin Ta'addanci, An Shirya Daukar Matakai

  • Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ( EFCC) ta dora alhakin ta'addanci a Najeriya a kan talauci
  • Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa za su rika sa ido kan hada-hadar bankuna
  • Olukoyede ya ce za a dauki matakin ne domin gano yan ta'adda da sauran bata-garin da ke musayar kudade ta banki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta bayyana cewa talauci da cin hanci sun taimaka wajen ta'addanci.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya ce hukumarsu za ta dauki matakan hana yan ta'adda da sauran bata-gari samun kudi.

Kara karanta wannan

"Mun san da baragurbi a cikinmu:" Rundunar sojoji ta fadi kokarinta kan rashin tsaro

Olukoyede
Ta'addanci: EFCC za ta sa ido kan bankuna Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Mista Olukoyede ya bayyana fargabar matasan kasar nan da ba su da aikin yi na cikin hadarin shiga harkar ta'addanci da garkuwa da mutane.

Hukumar EFCC ta fadi dalilin ta'addanci

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa hukumar EFCC ta ce akwai alaka mai karfi tsakanin talauci, cin hanci da rashawa da ta'addancin da ake fama da shi a Najeriya.

Mista Olukoyede wanda ya samu wakilcin daraktan yada labaran hukumar, Wilson Uwujaren ya ce za a iya amfani da talaucin wajen shigar da matasa satar mutane.

Ta'addanci: Matakin da EFCC za ta dauka

Shugaban EFCC na kasa, Ola Olukoyede ya ce za su fara sanya idanu kan yadda ake cinikayya a bankuna da zummar kama bata-gari da yan ta'adda.

Ya ce ta haka ne za a iya bibiyar miyagun yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka a kasar nan domin shawo kan matsalar da ake ciki.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya koka da sace mutane a asibitin Kaduna, ya fadi abin da ake bukata

EFCC ta gano masu ta'azzara laifuffuka

A baya kun ji cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta ce akwai sarakunan da ke da hannu wajen hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana haka, inda ya ce duk da illar hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, amma sarakunan na ba masu aikin hadin kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.