Sojoji Sun Kutsa cikin Daji, Sun Hallaka Ƴan Bindigar da Suka Addabi Mutane a Arewa

Sojoji Sun Kutsa cikin Daji, Sun Hallaka Ƴan Bindigar da Suka Addabi Mutane a Arewa

  • Sojoji sun hallaka ƴan bindiga huɗu, sannan sun kuɓutar da mutum bakwai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna
  • Rahotanni daga mazuana yankin Kasangwai sun nuna cewa sojojin sun farwa ƴan bindigar ne a maboyarsu ta jeji ranar Litinin da ta gabata
  • Har yanzu ba a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Hassan Mansur ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Ƴan bindiga huɗu sun bakunci lahira, mutum bakwai da aka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar ƴanci a lokacin da sojoji suka kai samame sansanin ƴan bindiga a Kaduna.

Dakarun sojojin sun samu wannan nasara ne a sansanin ƴan bindiga da ke jejin Kasangwai a ƙaramar hukumar Kagarko.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kai ɗauki, wa'adin biyan 'harajin N30m' ga Bello Turji ya cika a Zamfara

Malam Uba Sani.
Sojoji sun halaka mutum 4 da suka kai samame maboyar ƴan bindiga a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Yadda sojoji suka farwa ƴan bindiga

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin yankin, Labaran Shehu na cewa dakarun sojojin sun dura kan ƴan bindigar ne da yammacin ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, wasu mafarauta mutum biyu ne suka jagoranci sojojin zuwa cikin dajin da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Litinin.

Labaran ya kuma tabbatar da cewa jami'an tsaron sun ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su.

Ya ce waɗanda aka kubutar sun haɗa da mata guda biyu kuma bayanai sun nuna maharan sun sace su ne a kauyen Sardauna, mai maƙwaftaka da Kasangwai.

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan bindiga Kaduna

Wani shugaban al’umma da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun ja da baya, sun arce domin tsira da rayuwarsu bayan sojoji sun ci karfinsu.

Kara karanta wannan

DHQ: Ƴan ta'adda sama da 120,000 sun ajiye makamai, sun miƙa wuya ga sojojin Najeriya

Har kawo yanzu ba a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanndan Kaduna, ASP Hassan Mansur kan wannan hari ba.

DHQ ta faɗi adadin ƴan ta'addan da suka miƙa wuya

A wani rahoton kuma, hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa zuwa yanzu ƴan ta'adda akalla 125,517 sun miƙa wuya ga dakarun sojoji.

Shugaban sashen ayyuka na DHQ, Manjo Janar Emeka Onumajuru ya ce sojoji sun samu nasarar magance ayyukan ƴan ta'adda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262