Shugaba Tinubu Ya Turawa Gwamnoni Sama da N100bn bayan Abin da Ya Faru a Maiduguri

Shugaba Tinubu Ya Turawa Gwamnoni Sama da N100bn bayan Abin da Ya Faru a Maiduguri

  • Yayin da ruwa ke ci gaba da ambaliya, Bola Ahmed Tinubu ya ba kowace jiha N3bn domin ɗaukar matakin kariya
  • Shugaban ƙasar ya amince da ba jihohi N109bn domin magance ƙalubalen ambaliya da zaizayar ƙasa da tallafawa al'umma
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ruwa ya yi ambaliya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba gwamnonin jihohi kuɗi N108bn domin yaƙi da masifu kamar ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa.

Hakan na nufin kowace jiha daga cikin jihohi 36 za ta samu N3bn domin magance irin waɗannan bala'o'i idan suka taso

Shugaba Tinubu.
Tinubu ya bai wa jihohi N108b don magance ambaliyar ruwa da zaizayar kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wannan mataki da Bola Tinubu ya ɗauka na zuwa ne a daidai lokacin da ruwa ke ci gaba da yin ambaliya a jihohin Arewa, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Yadda ake fama da ambaliya a Najeriya

Baya ga jihohin Arewa, hasashen yanayi ya nuna cewa jihohi da dama a kudancin Najeriya na iya wayar gari a cikin matsalar ambaliyar ruwa.

Bayan ambaliyar ruwa, zaizayar kasa na ƙara ƙaruwa fadin kasar nan, musamman a yankin Kudu maso Gabas.

Haka zalika jihar Kaduna da ke Arewa maso Yamma tana fama da ibtila'in zaizayar ƙasa a ƴan kwanakin nan.

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ƙarin ruwan sama da kuma yiyuwar ambaliyar ruwa yayin da shekarar 2024 ta zo ƙarshe.

Gwamna Zulum ya karbi N3bn daga Tinuɓu

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum, ya tabbatar da cewa ya karbi Naira biliyan uku daga gwamnatin tarayya domin tallafawa waɗanɗa ambaliya ta rutsa da su.

Zulum ya karɓi tallafin gwamnatin tarayya ne a daidai lokacin da ruwa ya ɓalle daga Alau Dam, ya mamaye Maiduguri da wasu wurare.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya bayyana adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno

A cewarsa, mutane fiye da miliyan daya ne suka rasa matsugunansu sakamakon wannan ambaliya, in ji Channels tv.

Bisa haka ne shugaban ƙasar ya turawa kowane gwamna N3bn domin ɗaukar matakan kariya da kuma tallafawa waɗanda ibtila'in ya rutsa da su.

Ruwa ya fara janyewa a Maiduguri

A wani rahoton na daban wasu daga cikin mazauna Maiduguri sun fara ƙoƙarin komawa gidajen su bayan ruwan ambaliya ya janye da safiyar ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin sun fara tantance asarar da suka yi sakamakon ibtila'in wanda ya mamaye yankuna da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262