"Na Yi da Shekau Ma": Bulama Bukarti Ya Yi Martani bayan Bello Turji Ya Gargade Shi

"Na Yi da Shekau Ma": Bulama Bukarti Ya Yi Martani bayan Bello Turji Ya Gargade Shi

  • Bayan sabon bidiyo da Bello Turji ya yi yana gargadin Audu Bulama Bukarti, lauyan ya yi martani ga dan ta'addan a yau Laraba
  • Bukarti ya kalubalanci Turji inda ya ce a baya shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi masa barazana irin haka
  • Lauyan ya bukaci gwamnati ta ci gaba da dagewa wurin tabbatar da ta kawo karshen matsalolin yan ta'adda da sauran laifuffuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Fitaccen lauya, Bulama Bukarti ya yi martani bayan sabon bidiyon Bello Turji da ya ke yi masa gargadi.

Bukarti ya ce barazanar Bello Turji ba za ta taba karya masa guiwa ba inda ya ce zai cigaba da fadan gaskiya a kansu.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya yi sabon bidiyo, ya tura sako ga Pantami, Dan Bello da malamin Musulunci

Bulama Bukarti ya caccaki Bello Turji bayan ya yi masa gargadi a wani bidiyo
Bulama Bukarti ya mayarwa Bello Turji martani. Hoto: Audu Bulama Bukarti.
Asali: Facebook

Bulama Bukarti ya yi martani ga Bello Turji

Lauyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X a daren yau Laraba 11 ga watan Satumbar 2024.

Bukarti ya ce Turji ya yi hakan ne domin yi masa barazana da kuma kashe masa guiwa kan abin da yake yi.

Ya ce hakan da ya yi ba zai taba cin nasara ba inda ya ce ya sha barazana sosai a baya daga shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.

Bulama Bukarti ya ja kunnen Bello Turji

"Turji ya yi hakan ne domin ya yi mani barazana amma kuma hakan ba zai yi nasara ba, wannan ba shi ne karon farko da ake yi min barazana ba."
"Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi irin haka amma ban gajiya ba kuma yanzu ma ba zan yi ba, Shekau ya tafi kuma da yardar Allah Turji zai tafi nan ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace Bello Yabo? Shehi ya yi maganar 'garkuwa' da shi da 'kamen' DSS

"Yan ta'adda kamar Turji suna cigaba da sace mutane da kisa da kuma cin zarafin mata, yanzu yana harin mai neman zaman lafiya da kokarin samar da ingantaccen mulki kamar ni."

- Bulama Bukarti

Bello Turji ya gargadi Bulama Bukarti

A labari mai kama da wannan, kun ji cewa dan ta'adda, Bello Turji ya sake fitar da bidiyo kan fitaccen lauya, Bulama Bukarti bayan fitar da wani rahoto.

Bello Turji ya soki Bukarti inda ya ce rahoton da ya fitar akwai son rai a ciki ya kamata ya ji ta kowane bangare domin yin alkalanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.