Sojoji Sun Kai Ɗauki, Wa'adin Biyan 'Harajin N30m' ga Bello Turji Ya Cika a Zamfara

Sojoji Sun Kai Ɗauki, Wa'adin Biyan 'Harajin N30m' ga Bello Turji Ya Cika a Zamfara

  • Mutanen garin Moriki a ƙaramar hukumar Shinkafi sun fara zaman ɗar-ɗar bayan sun kasa biyan Bello Turji N30m da ya nema
  • Yayin da wa'adin da ƙasurgumim ɗan bindigar ya bayar ke cika, an ƙara girke dakarun sojoji da askarawan Zamfara a garin
  • Wani mazaunin Moriki ya ce duk da wannan mataki na turo sojoji suna jin tsoro saboda ƴan bindigar ba su da imani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Rahotanni sun nuna cewa an ƙara tura dakarun sojoji zuwa garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.

Hakan na zuwa ne bayan wa'adin da ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji ya ba mazauna garin su biya harajin N30m ya cika.

Kara karanta wannan

NAF: Jirgin sojoji ya yi luguden wuta kan ƴan bindiga, ya hallaka da dama a Arewa

Sojojin Najeriya.
An kara girke sojoji da askarawa bayan lokacin da Bello Turji ya buƙaci a biya haraji ya wuce a Zamfara Hoto: HQ Nigeria Army
Asali: Facebook

Meyasa Bello Turji ya ƙaƙaba harajin N30m?

Bello Turji ya kaƙabawa mutanen garin Moriki harajin N30m bayan sojoji sun kashe wasu shanunsa 100 makonni uku da uka shige, rahoton Daily Trust.

An samu labarin cewa sojoji sun kama shanun ne a Dumfawa, wani kauye tsakanin Moriki da garin Shinkafi a wani lokaci cikin watan Agusta.

Sojoji sun dura garin Moriki

Da yake tabbatar da lamarin, wani mazaunin garin, Aminu Musa, ya ce sun ga an ƙara girke dakarun sojoji a yankin.

"Baya ga sojojin, gwamnatin Zamfara ta turo askarawa (CPG) zuwa garin domin taimakawa jami'an tsaro.
"Mun ji daɗi saboda ganin jami'an tsaro ya kwantar mana da hankali. Wani kwamandan sojoji ya tabbatar da za su bamu kariya iya ƙarfinsu."

Wane hali mazauna Morki ke ciki?

Wani mazaunin garin Iliyasu Ali, ya ce duk da karin jami’an tsaro da aka tura, mutanen garin na cikin danuwa da fargabar abin da ka iya faruwa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa cikin daji, sun hallaka ƴan bindigar da suka addabi mutane a Arewa

"Har yanzu mutane na fargaba saboda ɓarayin nan ba su da imani, za su iya tunkarar sojoji, suna da manyan makamai fiye da sojoji.
"Wannan ya sa mutane suke tsoro saboda wa'adin biyan harajin ya ƙare daga yau, Allah ƙaɗai ya san abin da zai faru.
"Mun kasa biyan harajin kuma Turji ya yi alƙawarin tarwatsa garin nan idan muka gaza biyan diyyar shanunsa.

Kokarin jin ta bakin dagacin kauyen Moriki, Alhaji Bashar Isma’il Ari, ya ci tura saboda wayarsa tlna kashe a lokacin da aka tuntube shi, rahoton Punch.

Babban hafsan tsaro ya sha alwashin kama Turji

Ku na da labarin babban hafsan tsaro na ƙasa Christopher Musa ya sha alwashin kama Bello Turji wanda ya addabi mutanen jihar Zamfara.

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa nan da ɗan ƙanƙanin lokaci za a cafke jagoran 'yan ta'addan da ke Arewa ta yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262