Kano: Dan a Mutun Kwankwaso Ya Yi Murabus, Ya Ajiye Mukaminsa a Gwamnatin Abba
- Babban mai tallafawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan harkokin rediyo, Abdullahi Tanka Galadanchi ya yi murabus daga aikinsa
- An rahoto cewa Abdullahi Galadanchi ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Kano saboda zargin rashin iya aiki da makauniyar soyayya
- Galadanchi ya gargadi Sanata Rabiu Kwankwaso da ya kiyayi mutuwar kaskon da ya ke kira domin da alama ya fada da bakin Mala’iku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Babban mai tallafawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan harkokin rediyo, Abdullahi Tanka Galadanchi ya watsar da tafiyar siyasar gidan Sanata Rabiu Kwankwaso.
Abdullahi Tanka Galadanchi, wanda aka shaida ya na daya daga cikin 'yan a mutun Kwankwasiyya ya jiye mukaminsa a gwamnatin Kano.
Hadimin Abba ya yi murabus
A zantawarsa da gidan rediyon Freedom, Abdullahi Galadanchi ya nuna cewa akwai rashin iya aiki a tattare da gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
An ce Galadanchi ya bayyana cewa ba zai ci gaba da yiwa gwamnatin Abba aiki ba alhalin jagoran Kwankwasiyya wulakanta mabiyansa.
"Jagora bai rantse zai gudanar da lamuran jihar Kano a yanzu ba. Mun san cewa gidansa ne kuma kamfaninsa ne, amma ba a ce wanda ka samawa aiki ya zama bawa ba."
- Inji Galadanchi.
Galadanchi ya soki Kwankwaso
Galadanchi ya zargi jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa da wofantar da masu yi masa biyayya yana mai cewa Kwankwaso ba ya son taimakon kowa.
Tsohon mai taimakawa gwamnan Kano ya ce ba zai yiwu a ce mutum daya ya zama shi ne ke tafiyar da ragamar komai na gwamnatin jihar ba.
Ya gargadi Kwankwaso da ya kiyayi mutuwar kaskon da ya ke yawon ambata "domin da alama ya fada da bakin Mala’iku."
"Ba zai yiwu kana jagora kana wofantar da wanda suke kaunarka ba. Ba ka jawo wadanda suke sonka a jikinka domin su ne za su iya jibinci lamarinka ko da wata tababa ta faru."
- A cewar Galadanchi.
Duba hirar a nan kasa:
Asali: Legit.ng