'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Harin Ta'addanci a Jihar Neja

'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Harin Ta'addanci a Jihar Neja

  • Ƴan ta'adda waɗanda ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai harin ta'addanci a garin Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun kai harin ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 11 ga watan Satumban 2024
  • Jami'an tsaro waɗanda suka yi musayar wuta da miyagun ƴan ta'addan sun buƙaci mutanen garin da su yi zamansu a cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu ƴan ta’adda da ake zargin ƴan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a jihar Neja.

Ƴan ta'addan sun kai harin ne a garin Bassa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

'Yan ta'adda sun kai hari a Neja
'Yan ta'adda sun sake kai hari a Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan ta'adda sun kai hari a Neja

Kara karanta wannan

An yi rashi: Direban mota ya hallaka babban jami'in 'dan sanda

Majiya mai tushe da ke kusa da ƙauyen ta shaidawa jaridar Premium Times cewa tun da ƙarfe 5:30 na safiyar ranar Laraba suke ta jin ƙarar harbe-harbe daga yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A lokacin da aka fara kai harin da safiyar yau, jami’an tsaro sun ce mutane su zauna a gida yayin da suke musayar wuta da maharan."

- Wata majiya

Ƴan ta'adda na yawan kai hari a yankin

Garin Bassa ya daɗe yana fama da hare-haren ƴan Boko Haram waɗanda suke samun mafaka a dajin Allawa da ke kusa da garin.

A ɗaya daga cikin hare-haren da aka kai garin a farkon wannan shekarar, ƴan ta'adda sun kashe wasu sojoji ciki har da wani mai matsayin Kyaftin.

Wannan harin ya kai ga janye jami'an sojojin daga garin.

A kwanan nan ne mazauna garin suka koma Bassa bayan da gwamnati ta tura jami’an tsaro na haɗin gwiwa domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Kara karanta wannan

Babban alkali ya kubuta daga hannun 'yan ta'adda bayan kwashe watanni a tsare

Alƙali ya kuɓuta daga hannun ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa alƙalin babbar kotun jihar Borno, Haruna Mshelia, wanda ƴan ta'adda suka yi garkuwa da shi ya kuɓuta.

Wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne suka yi garkuwa da Haruna Msheila a ranar 24 ga watan Yuni tare da matarsa da direbansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng