Borno: Ambaliya Ta Kashe 'Yan Boko Haram Sama da 100 a Sambisa

Borno: Ambaliya Ta Kashe 'Yan Boko Haram Sama da 100 a Sambisa

  • Ana cigaba da samun rahotanni kan yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa ambaliyar ta kashe yan Boko Haram sama da 100 a dajin Sambisa yayin da ruwan ya afka musu
  • Haka zalika ruwan ya yi wa yan Boko Haram barna sosai inda ya tilasta musu sakin wadanda suka kama da karfin tsiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rahotanni na nuni da cewa ambaliyar ruwa da aka yi a jihar Borno ta shafi yan ta'addar Boko Haram sosai.

An ruwaito cewa yan ta'addar sun tafka asarar rayuka da kuma dukiya mai dimbin yawa a dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Borno: Mutanen Maiduguri sun wayi gari da labari mai daɗi bayan ambaliyar da ta afku

Ambaliyar ruwa
Ambaliya ta kashe Boko Haram a Borno. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ruwan ya fatattaki wasu yan ta'addar Boko Haram da suka yi mafaka a yankin Gwoza.

Ambaliya ta kashe Boko Haram a Borno

Rahotanni na nuni da cewa ambaliyar ruwa da aka yi a Borno ta kashe yan Boko Haram sama da 100 a dajin Sambisa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa da misalin karfe 2:00 na dare ruwan ya mamaye maboyar yan ta'addar suna barci kuma ya kashe su.

An samu rahotanni kan cewa wadanda suka mutu sun hada da mayakan Boko Haram, matansu da kuma ƴaƴansu.

Boko Haram sun saki mutane a Borno

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa ruwan ya wargaza wajen da Boko Haram suka daure mutanen da suka kama.

Hakan ya jawo yan ta'addar Boko Haram sun saki wasu daga cikin mutanen da suka tsare a dajin Sambisa bisa zalunci.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa da aka wayi gari da su a Maiduguri bayan ambaliya

A wani bangaren, an ruwaito cewa ambaliyar ta jawo tashin wasu mayakan Boko Haram a wasu yankunan Gwoza a jihar Borno.

Ambaliya: Mutane sun rasa gidaje a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa bayanai sun fara fitowa kan irin asarar da aka tafka a Maiduguri sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin.

Rahotanni da suka fito a safiyar yau na nuni da cewa mutane sama da 200,000 ne suka rasa gidajen zamansu sakamakon ambaliyar ruwan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng