Rikici bai Kare ba: Za a kai Shugaban Kwadago Asibiti bayan Kamun DSS

Rikici bai Kare ba: Za a kai Shugaban Kwadago Asibiti bayan Kamun DSS

  • Kungiyar kwadago ta bayyana cewa za ta kai shugabanta na kasa, Joe Ajaero asibiti domin duba lafiyarsa bayan an kama shi
  • NLC ta kuma yi Allah wadai da rike wasu takardun shugabanta masu muhimmanci da hukumomin Najeriya suka yi
  • Jami'an DSS sun kama shugaban NLC ne a filin jirgin sama yayin da yake kokarin tafiya Birtaniya halartar taron yan kwadago

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta sake fitar da bayani kan kama shugabanta da jami'an DSS suka yi a birnin tarayya Abuja.

Yan kwadagon NLC sun ce dole za su kai shugabansu, Joe Ajaero asibiti domin tantance halin da yake ciki.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin duniya sun taso Tinubu a gaba, za a gudanar da zanga zanga a kasashe

Shugaban kwadago
NLC za ta kai shugabanta asibiti. Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Jaridar the Sun ta wallafa cewa NLC ta sake fitar da sanarwar ne bayan jami'an DSS sun saki shugaban yan kwadago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama shugaban kwadago a Abuja

Legit ta ruwaito cewa DSS sun kama shugaban kwadago ne a filin jirgin sama yayin da yake shirin yin tafiya.

Kungiyoyin kwadago a ciki da wajen Najeriya sun yi Allah wadai da kama Joe Ajaero da jami'an DSS suka yi.

Za a kai shugaban kwadago asibiti

Biyo bayan sakin Joe Ajaero, NLC ta bayyana cewa dole za ta kai shi asibiti domin gwajin lafiyarsa.

NLC ta ce hakan ya zama dole ne domin a tabbatar da cewa babu wani abu na cutarwa da ya samu Joe Ajaero a hannun DSS.

An kwace takardun tafiyar Joe Ajaero

NLC ta bayyana cewa a lokacin da aka kama Joe Ajaero a filin jirgin sama an kwace masa takardun tafiye tafiye.

Kara karanta wannan

DSS ta tsorata, ta saki Ajaero mintuna kafin wa'adin kungiyar NLC ya cika

A karkashin haka, ƙungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin takardun domin ba Joe Ajaero damar yin tafiye tafiye.

NLC ta bukaci rage kudin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yi magana bayan shiga ganawar gaggawa da ta yi a kan kama shugabanta, Kwamared Joe Ajaero.

An ruwaito cewa yan kwadago sun fitar da sababbin bukatu hudu ga gwamnatin tarayya ciki har da rage kudin fetur da aka kara a makon jiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng